✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Zan fatattaki zaman kashe wando muddin kuka zabe ni – Peter Obi 

Ya bayyana haka ne a fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya

Dan takarar Shugaban Kasa na jamiyyar LP, Peter Obi ne ya yi alkawarin magance zaman kashe wando tare da farfado da sana’o’i musamman a tsakanin matasan kasar nan muddin ya dare karagar Shugabancin Najeriya a 2023.

Ya bayyana haka ne ranar Litinin a Fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya a Jihar Kaduna, lokacin da ya jagoranci wata tawagar jiga-jigan jam’iyyar wajen kai gaisuwa ga Sarki Ahmad Nuhu Bamalli.

Dan takarar, wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambra ne ya ce harkar noma ma za ta samu tagomashi domin ita ce babbar sana’ar da za ta taimaki a’’umma da kasa baki daya.

Ya ce Arewacin Najeriya na da kyakkyawan yanayi da kuma fadin kasa mai yalwa wanda idan aka samar da ingantaccen tallafi ga manoma, Najeriya za ta yi tunkaho da noma.

Peter Obi tare da Sarkin Zazzau a fadarsa da ke Zariya
Peter Obi tare da Sarkin Zazzau a fadarsa da ke Zariya

Obi wanda mataimakin takararsa, Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi wa rakiya, ya shawarci ’yan Nijeriya da su guji siyasar kabilanci da bangaranci da kuma addinanci.

Ya ce, “Masu amfani da wannan, suna yi domin raba kan ’yan Nijeriya da kokarin kawo rashin zaman lafiya a tsakanin al’ummomi da ke zaune tare da juna na tsawon lokaci.

“Yanzu da ake fuskantar zabe ne ya kamata ku fatattaki irin wadannan ’yan siyasa ta hanyar amfani da kuri’ar ku wajen zaben ’yan takara na gari da za su taimakawa rayuwarku,” in ji shi.

Tun farko a jawabinsa, dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa a jam’iyyar ta LP, Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya ce ziyarar tasu ta neman tabarruki ce musamman kasancewar shi dan gida kuma haifaffen Zariya.

Ya ce lokaci ya yi da jama’a za su yi hobbasa wajen zaben shugabanninsu da kansu ba tare da jiran wani ya juya akalarsu ta inda yake so ba.

Datti Baba Ahmed ya kara da cewa, al’umma ya kamata su kalli takarar su ba ta bangaren addini ko kabila ba, sai dai ta hanyar fahimtar cewa takara ce ta ’yan Najeriya masu ra’ayin kwato ’yancin ’yan kasa da kuma tsarkake ta.

Da yake mayar da jawabi, Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli ya nuna farin cikinsa bisa ziyarar da aka kawo, inda ya hori dukkan ’yan siyasa da su sanya bukatun ’yan kasa a gaban nasu.