✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Zawarcin Kwankwaso da APC ke yi ya tayar da kura

Majiyar Aminiya ta tabbatar cewa Buni da Osinbajo na tattaunawa da Kwankwaso dn ganin ya dawo APC

Uwar jam’iyyar APC mai mulki ta shiga zawarcin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, gabanin zaben 2023.

Aminiya ta gano cewa bangaren Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da kuma Shugaban Riko na APC, Mai Mala Buni, sun tuntubi Kwankwaso domin ganin ya dawo jam’iyyar gabanin zaben.

“Ana tattaunawa tsakanin oga da su, suna so ya dawo APC, amma yana nazari tukuna, har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba ,” inji wata majiya mai kusanci da Kwankwaso.

Kawo yanzu dai Kwankwaso bai riga ya sanar da matsayinsa game da neman takarar Shugaban Kasa ba a zaben na 2023, ko da yake ya nemi takarar a zabukan 2015 da 2019; La’alla saboda rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyarsa ta PDP.

A shekarar 2019 ne dai Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar APC, gabanin zaben shugaban kasa, inda ya nemi tikitin takarar Shugaban Kasa a PDP, amma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya kayar da shi da Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwa, wanda ya zo a matsayi na biyu a zaben fid-da-gani.

A bangaren jam’iyyar APC mai mulki kuma, tuni dai kusoshinta suka shiga lissafi, tun bayan da jagoran jam’iyyar na Kasa, Bola Tinubu, ya sanar da aniyarsa ta neman takarar Shugaban Kasa a zaben 2023.

Kawo yanzu dai Osinbajo dai bai riga ya bayyana matsayinsa game kan takarar shugaban kasa a 2023 ba.

Sai dai kuma wata majiya mai karfi daga cikin makusantansa ta shaida mana cewa tafiya ta yi nisa a game da neman takarar tasa.

Har yanzu dai Kwankwaso bai fito ya ce uffan ba, yana kan duba damar da ke akwai a zaben na 2023 ta fuskoki da dama tukuna.