✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

6 ga Mayu ne sabon wa’adin hada lambar waya da NIN

Kawo yanzu an hade layukan wayan mutum miliyan 51 da lambobinsu na NIN

Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami ya sanar da kara wa’adin da Gwamnatin Tarayya ta sanya na hada layukan waya da lambar shaidar dan kasa na NIN zuwa ranar 6 ga watan Mayu, 2021.

Pantami ya sanar a ranar Juma’a cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da bukatar hakan da kwamitin aiki da cikawa da yake jagoranta mai lura da aikin ya gabatar masa.

Pantami ya ce “An yi zaman a ranar Alhamis 1 ga Afrilu, 2021 inda aka amince da kara wa’adin hade layukan waya da lambar NIN zuwa ranar 6 ga Mayu, 2021, bayan amcinewar Shugaba Buhari da bukatar hakan da aka gabatar masa”.

Sanarwar da ma’aiktar ta fitar ta ce yanzu yawan masu rajistar NIN a duk wata ya karu zuwa mutum miliyan 2.6 a cikibiyo 3,800 da ke fadin Najeriya.

Ta kara da cewa kawo yanzu mutum miliyan 51 sun samu lambobinsu na NIN a fadin Najeriya, wansu dama kuma sun kusa kammala rajista inda suke jiran samun lambobinsu na NIN.

“Kasancewa kowane mutum na da layin waya 3 zuwa 4, yawan lambobin NIN zai cike gibin da ake da shi na yawan layukan wanyan da ke kasa,” inji shi.

Da yake jawabi, Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ce hade layukan waya da NIN zai taimaka wajen bibiyar ayyukan ’yan damfara da dangoginsu.