✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

7 daga cikin kowane yaro 10 a Jigawa na rayuwa cikin kangin talauci – UNICEF

UNICEF ta bayyana hakan ne a cikin wani rahoton da ta gabatar kan jihar

Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce jihar Jigawa ce ke kan gaba a jihohin da ke fama da talauci a Najeriya inda kaso 73.9 na yaran jihar ke rayuwa cikin kangin fatara.

Bayanin hakan na kushe ne a cikin wani rahoto na sakamakon bincike mai lakabin MICS 6 da asusun ya gudanar a Kananan Hukumumomin jihar 27 a shekarar 2021.

A jawabinsa yayin taron gabatar da rahoton, mai kula da ofishin shiyya na asusun a Kano, Rahama Mohammed Farrah ya ce, rahoton sakamakon binciken na da matukar tayar da hankali.

Ya ce rahoton ya nuna karara irin mummunan halin rayuwar yara a jihar ke ciki, da kuma yadda za  su  kasance nan gaba.

“Yawancin yara a jihar an hana su hakkin da su ke da shi na rayuwa mai kyau da kariya da kuma ci gaba mai amfani,” inji Rahama

Rahoton ya kuma nuna cewa kaso 65 na yara a jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya na cikin kangin fatara idan aka kwatantasu da sauran yaran da ke sauran sassan kasar.

Sai dai rahoton ya yaba wa jihar bisa nasarar da ta samu na riga-kafin yara a inda mace-macen da ake samu a cikinta ya ragu da kaso 37 a tsakanin yara ‘yan kasa da shekara biyar.