✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin PDP: Sau 5 na zauna da Wike don yin sulhu —Atiku

Atiku ya ce har yanzu Wike yaje jira, ya ji da wacce zai zo.

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce sau biyar yana ganawa da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, don kawo karshen matsalolin da ke tsakaninsu.

Atiku ya bayyana haka ne a wani taro da gidan talabijin na Channels ya shirya a daren ranar Lahadi.

“Na gana da Wike sau biyu a Fatakwal, sau biyu a Abuja sai kuma sau daya a Landan.

“Ba daga bangarena ba ne, daga daya bangaren ne; ina jiran sa na ji da wadda zai zo,” cewar Atiku.

Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasar bai bayyana abubuwan da suka tattauna da Wike a ganawar da suka yi ba.

Wike ya shiga takun saka da Atiku ne tun bayan kammala zaben fid-da-gwanin jam’iyyar PDP da ya gudana a watan Mayu, inda ya sha kaye a hannun Atikun.

Takun saka tsakaninsu ta yi tsami tun bayan da tsohon mataimakin shugaban kasar ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa maimakon Wike.

Tun daga lokacin gwamnan na Ribas ya ja layi da Atiku da kuma shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu.

Wike da wasu gwamnonin PDP hudu da ake wa lakabi da G-5 sun lashi takobin ganin bayan shugabancin Ayu.

A watan da ya gabata, Wike ya yi alkawarin mara wa ’yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun LP da NNPP, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso baya a zaben 2023.

Sai dai abin da ba a sani ba, shi ne ko Wike din zai yi wa jam’iyyarsa bore ya mara wa wani dan takara baya?