✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hotunan addu’ar ukun Sarkin Zazzau Shehu Idris

A ranar Laraba 23 ga Satumba, 2020 aka yi addu’o’i, kwanan uku bayan rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu yana da shekara…

A ranar Laraba 23 ga Satumba, 2020 aka yi addu’o’i, kwanan uku bayan rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu yana da shekara 84 a duniya bayan ya shafe shekara 45 a matsayin Sarkin Zazzau na 18.

Ga wasu hotunan da Aminiya ta tattaro muku na yadda addu’o’in suka gudana a Fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya:

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa wurin addu’ar ukun.
Obasanjo da El-Rufai da sauran mutane sun daga hannu a lokacin da ake gudanar da addu’ar
Wasu sarakuna da suka halarci taron addu’ar ukun da aka gudanar a ranar Laraba.
Obasanjo da El-Rufai sun daga hannu a lokacin da ake gudanar da addu’ar.
Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo yana jawabi a lokacin taron addu’ar ukun Sarkin Zazzau, Shehu Idris.
Daga hannun dama Obasanjo ne da Kayode Fayemi sanye da fararen kaya, sai tsohon Gwamnan Kaduna, Mukhatar Ramalan Yero da tsohom Mataimakin Shugaban Kasa Muhammad Namadi Sambo da sauran mahalarta.
Daga hannun dama Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti; tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo (a tsakiya) da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai (da shudin kaya).