✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka za ta fara kwashe jami’anta daga Najeriya saboda fargaba

Lai Mohammed ya ce babu abin da zai faru a Najeriya kowa ya kwantar da hankalinsa.

Kasa da sa’o’i 72 bayan fidda sanarwar yiwuwar kai hare haren ta’addanci a Abuja, babban birnin Najeriya, Amurka ta fara shirin kwashe jami’anta da iyalinsu daga kasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurkan ce ta bayyana wannan mataki cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

“A ranar 25 ga watan Oktoba ne muka sahale kwashe jami’an Diflomasiyya da sauran ma’aikatan Amurka da iyalansu daga Najeriya, sakamakon rahoton yiwuwar kai hari mai karfi da muka samu.

“Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja na ci gaba da samun takaitaccen ikon ba da agajin gaggawa ga ‘yan kasar Amurkan a Najeriya.

“Don haka ofishin Jakadancin Amurkan a Legas yana ba da duk taimakon gaggawar da Amurkawan ke bukata, da ma barin kasar,” a cewar sanarwar.

Sai dai duk da wannan gargadi da Amurkan ta yi, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ya ce tun watanni biyu da suka gabata jami’an tsaro suka fara daukar mataki kan lamarin.

“Duk wani zance da wata kasa za ta yi wa ‘yan kasarta, ba za ta yi wa gwamnatinmu tambari ba”, in ji shi.

Ya kuma nanata cewa kowa ya kwantar da hankalinsa, domin ‘yan kasar da ma wadanda ba ‘yan kasar ba, ba sa cikin wani hadari a Najeriya.