✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A aikace ya kamata a magance matsalar tsaro —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi ya ce a maganar fatar baki kan matsalar tsaro ta isa haka, saura aiki.

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce lokaci ya yi na shugabannin Najeriya su magance matsalar tsaro a aikace ba da maganar fatar baki ba.

Sarkin Musulmi ya ce ita matsalar tsaro tunkarar ta ake yi gadan-gadan ba da surutuan shugabanni da ’yan siyasa kan hanyoyin magance ta ba.

“Maganar fatar bakin ta isa haka, ku fito ku yi abin da kuke fada a aikace, saboda lokaci kawai ake kara batawa na magance matsalar a aikace,” inji Sarkin Musulmi ga taron da Majalisar Wakilai ta shirya kan tsaron kasa.

Ya shaida wa taron cewa,  “An dade ana ta maganar fatar baki, an yi a taron Kungiyar Gwamnonin Arewa, an yi a matakin tarayya, wanda kuma ni na jagoranta, amma maganar baka ce kawai.

“Ko a watannin baya mun yi ire-iren wannan taro da manyan shugabannin kasar nan, yanzu kuma ga shi muna sakewa, duk a kan matsalar tsaro. Saboda haka maganar fatar baki babu aiki ta isa haka.”

Ya ce a fili yake cewa al’amura sun dagule a Najeriya, “Na kuma ji dadi da ganin wasu daga cikin shugabanni sun fito sun fadi hakan a bainar jama’a.

“Mu daina yaudarar kanmu cewa abubuwan na tafiya daidai saboda  gaskiya abubuwa sun lalace, muna kuma ji, muna ganin shaidar hakan.”

Basaraken ya bayyana cewa sarakuna sun dade suna taka muhimmiyar rawa wajen hada kan jama’a, tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka da kafa Najeriya a matsayin kasa guda.

“Sarakuna abokan tafiyar shugabannin siyasa ne wajen kawo cigaban kasa, saboda haka mu ba gasa muke yi da su ba ta kowace fuska wajen gudanar da harkokin kasar nan.

“Mun yarda da sauyi, muna kuma karbar shi idan ya zo saboda Allah ne kadai ke kawo canji.”