✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A bai wa ’yan IPOB damar ballewa daga Najeriya — Nastura Ashir

Ba zai yiwu mutum ya ci gaba da zama da wanda ba ya son zama da shi ba.

Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula da ke Arewacin Najeriya, sun yi fatali da matakin dattawan Kudu maso Gabashin kasar da suka nesanta kansu daga kungiyar IPOB mai fafutikar kafa Kasar Biyafara.

A karshen makon ya gabata ne Gwamnonin Jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya suka yi Allah-wadai da masu fafutukar neman ballewa daga kasar, tare da nesanta kansu daga kungiyoyin na yankinsu da ma sauran dake wasu sassan Najeriyar.

Matakin Gwamnonin na zuwa ne bayan wani taro da suka gudanar a garin Enugu dangane da tashe-tashen hankulan da suka janyo hasarar rayuka da dukiya mai tarin yawa a Jihohin yankin nasu sakamakon hare-haren ’yan awaren haramtacciyar kungiyar IPOB mai neman ballewa daga kasar.

Sauran matakin da Gwamnonin suka zartar, akwai umartar matasan yankunansu da su kyale Dattijai su shige gaba wajen neman hakkokinsu daga Hukumomin Najeriya cikin ruwan sanyi.

Sun kuma yi kira ga sauran kungiyoyin yankunan Najeriya musamman na Arewacin kasar da su kai zuciya nesa gami da bai wa Kabilun Ibo mazauna yankunansu kariya daga duk wata barazana.

Sai dai duk wannan mataki, gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya ta yi zargin cewa babu gaskiya a cikinsa, lamarin da ta jaddada bukatar a bai wa matasan Kudu masu Gabashin kasar damar kafa tasu kasar.

Alhaji Nastura Ashir Sharfi, Shugaban Kwamitin Amintattau na Gamayyar Kungiyoyin, wanda ya zayyana hakan yayin ganawa da BBC Hausa, ya ce “ba zai yiwa mutum ya ci gaba da zama da wanda ba ya son zama da shi ba.”

“Maganar wai Gwamnonin yankin su fito su ce ba sa goyon bayan kafa Kasar Biyafara duk wasan yara ne, domin wadannan Gwamnonin su suka cusa wa matasan wannan akida ta kafa kasar Biyafara.”