✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘A binciko gwamnan da ke shugabantar Boko Haram’

Gwamnonin Arewa sun bukaci a binciki zargin da ake wa dayansu da zama shugaban Boko Haram

Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta bukaci hukumomin tsaro su binciki zargin da ake yi cewa “daya daga cikin gwamnonin Arewa ne shugaban kungiyar Boko Haram a Najeriya”.

Tsohon Mataimakin Babban Bankin Najeriya, Obadiah Mailafiya ya yi zargin, tare da cewa bakin ‘yan Boko Haram da ‘yan fashin daji da ke addabar Arewar daya.

Zargin da ya yi wa wani gwamna mai ci a yankin  a hirarsa da a wani gidan radiyo ya sa hukumar tsaro ta DSS gayyatarsa ya amsa tambayoyi kafin ta kayle shi a ranar Laraba a ofishinta na garin Jos, Jihar Filato.

Wata takarda da gwamnonin Arewa suka fitar a ranar ta nuan damuwa game da girman zargin wanda ta ce bai kamata a kyale shi hakan nan ba tare da an bincika ba.

“A matsayin Gwamnonin Arewa mun sha tattauna matsalar tsaro a yankin da ma kasa baki daya inda muka sha yin tir a ayyukan ta’addacin Boko Haram da ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane kadai ba.

“Mun kuma sha tattaunawa tare da Shugaban Kasa da shugabannin tsaro domin lalubo mafita daga matsalar.

“Zargin cewa daya daga cikinmu shi ne kwamandan Boko Haram zargi ne mai karfi da bai kamata a kawar da kai daga gareshi ba.

Taron Shugaba Buhari da shugabannin tsaro da gwamnonin Arewa kan matsalar tsaro

— ‘Muna fata ba zagon kasa ba ne’

“Muna kira da a gudanar da cikakken bincike a kan zargin”, inji Shugaban NGF, Gwamna Simon Lalong na Filato a cikin sanawarsu ta ranar Laraba.

Sun bukaci Obadiah Mailaifiya da duk wani mai bayanin da zai taimaka a kawar da ta’addanci a yankin da ya taimaka wa Gwamnati da hukumomin tsaro domin samun nasara.

Kungiyar ta ce tana fata zargin ba yunkuri ne na wofintar da kokarin da suke yi na kawo karshin matsalar tsaro a yankin ba.

Ta jaddada cewa ba za ta taba mara wa kungiyar tayar da kayar baya baya ba saboda su kansu ba su tsira ba, wanda harin da aka kai wa Gwamna Babagana Zulum na Borno shaida ne a kan hakan.

Shugabannin tsaro da Zulum
Gwamna Zulum da shugabannin tsaro a wurin taro kan tsaro a yankin Arewa maso Gabas

— Zargin Obadiah Mailafiya ya tayar da kura

A wata hira da aka yi da Obadiah Mailafiya da ta karade shafukan zumunta, ya ce yana daga cikin wandada suka sha zama tare da manyan kwamdodin Boko Haram da suka tuba kan yadda za a magance matsalar.

“Bari in bayyana wasu abubuwa domin wasunmu mu ma muna yin binciken sirri.

“Mun tattauna da ba sau daya ba da wasu mayan kwamnadojin Boko Haram da suka tuba.

“Sun gaya mana cewa wani gwamnan Arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya.

“Boko Haram da ‘yan bindiga bakinsu daya, suna da karfi kuma tsarinsu na da sarkakiya da wuyar ganewa.

“A cikin lokacin kullen nan jiragensu sun yi ta kai-komo suna dakon makamai da kudade da sauran bukatu zuwa sassa daban-daban tamkar babu dokar ta kulle.


— Hadarin da ke tafe

Mailafiya ya ce ayyukan miyagun “sun riga sun isa kudu. Babu inda babu su kuma sun gaya mana cewa idan sun gama kai hare-hare a kauyuka, za su shiga mataki na biyu.

“A matakin na biyu za su rika shiga birane suna kai hari suna kashe manyan mutane a gidajensu. Ina tabbatar maka, wannan shine tsarin su.

“Ina shaida maka cewa so suke zuwa shekarar 2022 su fara yakin basasa a Najeriya”, inji shi.

Shirin gidan radiyon ya kuma tambaye shi ko yana da tabbacin abun da ya fada. Sai ya ce, “Ina da digirin digirgir daga Jami’ar Oxford kuma ni kwararren ma’aikacin Babban Bankin Najeriya ne.

“Mu ba mu fadin shaci-fadi, saboda haka ka dauki abun da na fada maka da muhimmaci”.