✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘A biya MKO Abiola hakkokin tsohon shugaban kasa’

Iyalan Marigayi Moshood Abiola sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sanya shi a cikin jerin tsofaffin shugabannin kasar. Da yake rokon ga Shugaba Buhari, Jagoran…

Iyalan Marigayi Moshood Abiola sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sanya shi a cikin jerin tsofaffin shugabannin kasar.

Da yake rokon ga Shugaba Buhari, Jagoran iyalan Abiola, Cif Olanrewaju Abiola na neman a biya iyalan mamacin dukkan hakkokinsa na tsohon shugaban kasa tun daga 1993.

MKO Abiola shi ne ake kyautata zaton ya ci zaben Shugaban Kasa na ranar 12 ga watan Yuni 1993, wanda aka soke kafin a sanar da sakamakon.

Cif Olanrewaju wanda wa ne ga Moshood ya bukaci Buhari ya mika bukatarsu ga Majalisar Tarayya ta yi doka a kai.

A cewarsa sanya Moshood Abiola cikin sahun tsofaffin shugabannin na da muhimmanci wajen nuna wa shugabannin Najeriya amfanin jagoranci cikin zaman lafiya.

Iyalan Abiola sun kuma yaba da karramawar da Shugaba Buhari ya yi wa mamacin wanda suka ce shi ne karfin danginsu.

Buhari ya ba wa Marigayi Abiola lambar girma (GCFR) da ake ba wa shugabannin kasa, ya kuma mayar makamanciyar ranar zabensa (12 ga watan Yuni) Ranar Damokraydiyya. Buhari ya kuma sanya sunan MKO Abiola a wani babban filin wasa domin tunawa da shi.