✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A boye ake satar kudi a gwamnatin Buhari — Amaechi

Ana satar kudi salin alin sabanin yadda ake yi a fili a lokacin gwamnatocin da suka gabata.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ce jami’an gwamnati a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na satar dukiyar al’umma a boye.

Amaechi wanda ya bayyana haka a yayin wata hira da Aminiya, bai musanta zargin da wasu ke yi na cewar akwai jami’an gwamnati a mulkin Shugaba Buhari da suke facaka da dukiyar jama’a ba.

A cewar Ministan, tabbas ana satar kudi a gwamnatinsu amma ana yi ne salin alin sabanin yadda ake yi a fili a lokacin gwamnatocin da suka gabata.

Furucin Ministan na zuwa ne a yayin da yake jawabi dangane da salon mulkin Shugaba Buhari da kuma kwazonsa wajen riko da akalar jagoranci laakari da watanni 21 ya rage wa’adinta ya kare.

Ya ce, wannan gwamnatin da take ci ta APC ta yi iya bakin kokarin ta wajen dakile almubazzaranci da dukiyar jama’a da kuma hukunta wadanda suka yi rub da ciki a kan kudaden talakawa.

Tsohon Gwamnan Jihar Ribas ya ce, a shekarun da suka gabata, za ka ga mutane sun zama attajirai dare daya ba tare da an san su da wata sana’a ba, kuma babu wanda ya hukunta su, amma a karkashin mulkin Buhari irin haka ba ta faruwa.

Amaechi ya ce “cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a karkashin gwamnatocin Najeriya da suka shude.

“A gwamnatocin baya za ka ga mutane suna bushasha da dukiyar da ba a san inda suka samo ta ba a bainar jama’a.

“Amma a karkashin wannan gwamnati idan za ka yi sata sai dai ka yi ta a boye, kuma idan an kama ka, za ka fuskanci fushin hukuma.