✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A bude Obajana ba tare da bata lokaci ba –Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Jihar Kogi ta rufe masana'antar kan takaddamar mallaka

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a bude Masana’antar Simintin Dangote da ke Obajana a Jihar Kogi, ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnatin ta bayar da wannan umarnin ne a Taron Majalisar Tsaro da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa, ranar Juma’a, wanda Shugaban Buhari ya jagoranta.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Ministan Harkokin ’Yan sanda Mohammed Dingyadi da Ministan Harkokin Cikin gida Rauf Aregbesola da kuma Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor a jawabinsu ga manema labarai bayan taron.

Aregbesola ya ce, an cimma yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Jihar Kogi da kuma Kamfanin Dangote kan bukatar a bude kamfanin, suna mai kira ga dukkanninsu da su mutunta yarjejeniyar.

Ministan ya ce, Majalisar Tsaron ta bayar da umarnin bude kamfanin simintin tare da cewa, duk wata matsala tsakanin masu takaddama a warware shi ta hanyar shari’a. Burin gwamatin samar da aikin yi.

A baya dai Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayar da umarnin rufe kamfanin na Dangote a bisa wata takaddama da ta taso a tsakanin gwmanatin jihar da kamfanin Dangote kan mallakar masana’anatar simintin.