✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘A daina sayar da fili ga bare a Kano’

Abin da muke fadi shi ne, ita ma Kano tana da masu ita kuma babu maganar kabilanci illa gaskiya.

Kungiyar Tabbatar da Ci gaban Jihar Kano (KANO LEADS) ta nuna damuwa kan yadda jama’a ke sayar da filaye barkatai ga mutanen Kudancin kasar nan da wadansu baki daga kasashen waje, inda ta ce lamarin ba zai haifar wa Kano da mai ido ba.

Shugabar Kungiyar, Hajiya A’isha Dankani ce ta bayyana haka yayin da take tattaunawa da manema labarai a wajen taron kaddamar da shugabannnin kungiyar na Kananan Hukumomin jihar.

Kungiyar, wacce ake yi wa take da ‘Da Ruwana’ ta yi zargin cewa ana hada baki da wadansu shugabannin al’umma wajen sayar da filayen ga bakin da ba a san daga inda suke ba, wanda hakan na iya zama barazana ga al’umma a nan gaba.

“Kowa shaida ne game da yadda ake sayar da kasuwanninmu, an sayar da ’ya’yanmu, yanzu kuma ga shi an koma ana sayar da filayenmu.

“To ya zama wajibi mu fito mu yi magana domin idan ba mu yi ba, babu wanda zai yi a madadinmu.

“Wane ne zai iya zuwa Imo ko Enugu ya sayi fili? Amma don Kano ta zama juji sai kowa ya zo ya mallaki fili a cikinta?

“Abin da muke fadi shi ne, ita ma Kano tana da masu ita kuma babu maganar kabilanci illa gaskiya,” inji ta.

Ta ce, “Masu unguwanni da dagatai na da muhimmiyar rawar takawa wajen ciyar da Jihar Kano gaba.”

Har ila yau, shugabar ta ce kungiyarsu ta kulla aniyar kawar da dabi’ar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasan jihar.

Ta ce yawancin matasa suna jefa rayuwarsu cikin mawuyacin hali, ta yadda suke fadawa harkar shaye-shaye da ta’ammali da miyagun kwayoyi, wanda hakan ba zai haifar musu da komai ba illa barazana ga ci gaban rayuwarsu.

Ta yi kira ga masu ruwa-da-tsaki a dukkan matakai su sanya hannu domin tsamo matasa daga halin da suka jefa kansu.

Yawanci  mahalarta taron da suka tattauna da Aminiya sun yi dauki alkawarin kawo canji domin ganin Jihar Kano ta ci gaba.

“Dole idan muna son ci gaba sai mun dauki matsalolin sauran ’yan uwanmu sun zama namu,” inji wani da ya halarci taron.