✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A fara duban wata ranar Alhamis —Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmi da su soma duban…

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmi da su soma duban watan Ramadan daga ranar Alhamis 23 ga watan Afrilu wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban 1441 bayan Hijira.

An fitar da sanarwar Sarkin Musulmin ne a cikin wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban Kwamitin Duban Wata na Majalisar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaid, ya rattabawa hannu aka rabawa manema labarai, ya bukaci duk wani mutum ko al’ummar da suka ga jinjirin watan su kai labarin ga wani basarake na kusa da su domin tantance gaskiyar ganin kafin kawo maganar gaban Sarkin musulmi.

Sannan an raba lambobin wayoyin tafi da gidanka da mutum zai iya magana da kwamitin ganin wata kai tsaye.

Lambobin su ne kamar haka: 08037157100, 070674116900,  08066303077, 08036149757, 0803596532.