✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A fara duban watan Zul-Hijja daga ranar Asabar – Fadar Sarkin Musulmi

Ranar ita ce ta yi daidai da 29 ga watan Zulkida  na shekarar 1442 bayan Hijira.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmin Najeriya da su fara duban watan Babbar Sallah na Zul-Hijjah daga ranar Asabar, 10 ga watan Yulin 2021.

Sarkin, wanda kuma shine shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya ya ce ranar ita ce ta yi daidai da 29 ga watan Zulkida  na shekarar 1442 bayan Hijira.

Umarnin dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban Kwamitin da ke ba Fadar Shawara Kan Al’amuran Addini kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce duk wanda ya ga watan zai iya kai labari ga Hakimi ko Dagaci mafi kusa da shi domin sanar da mai alfarma Sarkin Musulmin.

Daga nan sai ya roki Allah ya taimaki Sarkin a wannan aikin da yake yi ya kuma daura shi kan daidai.

Watan Zul-Hijja dai shine wata na 12 a shekarar Musulunci wanda a cikinsa ne ake gudanar da bikin Sallar Layya da ma Aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Sai dai a bana ma kasar ta Saudiyya ta takaita adadin mutanen da za su gudanar da aikin hajjin zuwa 60,000 kacal, kuma suma dole su kasance mazauna cikin kasar saboda annobar COVID-19.