✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A gaggauta hukunta wadanda suka kashe Sheikh Aisami —JIBWIS

Muna yaba wa hukumar ’yan sanda da suka dauki mataki nan take na cafke sojojin da aka samu tare da gawarsa.

Kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah wa Ikamatis Sunna a Najeriya (JIBWIS), ta yi kira ga mahukuntan kasar da su gaggauta hukunta wadanda ake zargi da kisan fitaccen malamin addinin Islama a Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami Gashuwa.

Shugaban JIBWIS na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya yi kira ga mahukuntan kamar yadda wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Litinin ta nuna.

“Shugaban JIBWIS Sheikh Dokta Abdullahi Bala Lau ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta daukan mataki akan wasu sojojin Najeriya guda biyu da suka kashe daya daga cikin malaman kungiyar Sheikh Gwani Aisami da ke garin Gashua ta jihar Yobe.

“Muna yaba wa hukumar ’yan sanda da suka dauki mataki nan take na cafke sojojin da aka samu a daji wajen gawar marigayin,” in ji Sheikh Bala Lau.

Sheikh Bala Lau ya kuma ce babu shakka kungiyar ba za ta amince da wannan “ta’addanci ba,” yana mai cewa “sun zura ido da kunnuwa domin sauraron yadda za ta kaya wajen aiwatar musu da hukunci cikin gaggawa.”

Kakakin rundunar ’yan sanda a Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, wanda ya tabbatar da kama sojojin, ya kuma ce bayan kammala bincike zai yi karin bayani kan wannan al’amari.

A cewar DSP Dungus, yanzu haka an kama mutum biyu da suka yi ikirarin sojoji ne da ke aiki da Bataliya ta 241 a garin Nguru na jihar.

Ana zargin John Gabriel da Adamu Gideon da harbin fitaccen malamin sau biyu, inda ya mutu nan take, kuma maharan suka yi yunkurin guduwa da motarsa, kamar yadda kakakin ’yan sandan ya tabbatar.

Bayanai sun ce Aisami na hanyarsa ta komawa garin Gashuwa daga Kano ne a lokacin da lamarin ya faru, inda wani soja ya nemi ya rage masa hanya, daga bisani kuma sojan ya bindige malamin har lahira ya kuma yi yunkurin guduwa da motarsa.

A zantawar da DSP Dungus ya yi da BBC, ya ce Shehin malamin yana tuka motarsa ne a kan hanyar zuwa Gashua daga Nguru lokacin da wanda ake zargi, sanye da kayan gida, ya roke shi da ya rage masa hanya zuwa Jaji-Maji – duka a cikin jihar ta Yobe.

“Jim kadan kafin su isa Jaji-Maji, malamin ya tsaya zai yi fitsari,” a cewar DSP Dungus Abdulkarim.

“Dawowarsa cikin mota ke da wuya sai mutumin ya zaro bindigar AK-47 kuma ya harbe shi sau biyu.”

Abdulkarim ya kara da cewa mutumin ya yi yunkurin guduwa da motar malamin amma suka gaza saboda ta makale a cikin tabo.

“Sai ya kira daya wanda ake zargin wanda ya tuko wata motar daban zuwa wurin don ya taimaka masa. Cikin rashin sa’a sai birkin motarsa ya karye.

“Mutanen sun nemi taimakon wasu jami’an tsaro na sa-kai a Jaji-Maji. Lokacin da suka isa wurin sai suka tarar da gawar Goni Aisami.”