✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A guji yin zaben SAK a 2023 —Matasan Arewa

Kungiyar AYDA ta bukaci ’yan Najeriya su guji zaben kowane irin dan takara da sunan “SAK” a zaben 2023.

Kungiyar Bunkasa Cigaban Matasan Arewa (AYDA) ta bukaci ’yan Najeriya da su guji zaben kowane irin dan takara ko jam’iyya da sunan “SAK” a zaben 2023.

Jagoran kungiyar, Kwamred Imrana Wada Nas ya ce, “A maimakon haka ya kamata a maida hankali wajen zaben Nagari ba tare da la’akari da jam’iyya, ko kabila ko wani banbanci ba.”

Ya yi kiran ne a yayin da yake nuna tababar kungiyar kan shirin jam’iyyar APC mai mulki na gudanar da zaben shugabanninta na kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Kwamred Imrana Wada Nas ya bayyana kokwantonsu ne a wani taron ’yan jarida da kungiyar ta kira a yammancin Alhamis a Abuja.

Ya kuma yaba wa jam’iyyar adawa ta PDP bisa yadda ta gudanar da zaben shugabaninta na kasa cikin nasara “Ba tare da wata rigima ba.”

A daya bangaren ya ce, jam’iyyar APC tana da tarin matsaloli da ke bukatar magancewa gabanin yin zaben shugabannin, amma ba ta nuna alamar za ta yi hakan ba.

“Wannan ne karo na uku da jamiyyar APC take nuna za ta yi taronta na kasa, sai dai a zahirin gaskiya, ko a wannan karon babu wani abu da ke nuna aniyarta ta yin taron in banda sanar da ranar kawai,” inji shi.

Jagoran na kungiyar matasan Arewan wanda ya gabatar da kansa a matsayin mamba a Jam’iyyar PDP, ya bukaci al’umma da su yi fatali da zabar wata jam’iyya da sunan “SAK”.

“A maimakon haka ya kamata a maida hankali wajen zaben Nagari ba tare da la’akari da jam’iyya, ko kabila ko wani banbanci ba,” kamar yadda ya yi bayani.