✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘A hana masu taurin kai zuwa filin jirgi’

Malisar Wakilai ta bukaci a hana duk shugaban da ya ki bin matakan kariyar cutar coronavirus shiga filayen jiragen sama. Shugaban Kwamitim Majalisar kan Sufurin…

Malisar Wakilai ta bukaci a hana duk shugaban da ya ki bin matakan kariyar cutar coronavirus shiga filayen jiragen sama.

Shugaban Kwamitim Majalisar kan Sufurin Jiragen Sama Nnolim Nnaji ya yi kiran yayin nuna takaicin abin da ya ce na kunya ne yadda wasu gwamnoni da manyan mutane ke yi wa ma’aikata tirjiya wajen bin dokokin a filayen jiragen sama.

“Ba za mu bari ba mutum komai matsayinsa ya rika gangancin jefa rayukan ’yan Najeriya cikin halaka babu gaira babu dalili”, inji shi.

Nnaji ya ce majalisar na goyon bayan ma’akiatan Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama (FAAN) da na Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) wajen tabbatar da dokokin, “domin su ne a sahun gaba wajen yaki da cutar”.

Ya kuma ba su tabbacin goyon bayan Gwamnati Tarayya domin “ta kashe makudan kudade wajen tabbatar da matakan kafin bude tashoshin jiragen sama, saboda haka wajibi ne kowa ya bi su”, inji shi.

Shugaban kwamitin ya kirayi shugabannin hukumomin biyu da su ba wa ma’aikatansu kwarin gwiwa, musamman jami’an lafiya da na tsaro wajen zartanar da hukuncin hana duk wanda ya yi taurin kai wuce.

Ya ce rashin yin hakan ne zai kara jefa ma’aikatan da ma sauran masu amfani da filayen jiragen cikin hadarin kamuwa da cutar.