✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A hukunta wadanda suka soke zaben 1993 — Balarabe Musa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa ya bukaci Shugaba Buhari ya binciki soke zaben shugaban kasa na 1993 da Gwamnatin Babangida ta yi. Balarabe…

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Abdulkadir Balarabe Musa ya bukaci Shugaba Buhari ya binciki soke zaben shugaban kasa na 1993 da Gwamnatin Babangida ta yi.

Balarabe Musa ya zargi soke zaben na ranar 12 ga watan Yuni 1993, da haifar da matsalolin da Nejeriya ke ciki a yanzu, don haka ya kamata a hukunta wadanda suka soke shi.

A jawabinsa na zagayowar Ranar Damokradiyya ta 2020, Balarabe Musa ya ce karrama Cif MKO Abiola da ya lashe zaben da kuma ayyana 12 ga wata Yuni a matsayin Ranar Damokradiyya kadai bai wadatar ba.

Dole Buhri ya karashe aikin a yi bincike a kuma hukunta wadanda suka soke zaben domin zama izina a nan gaba.

“Matukar Buhari bai yi fiye da hakan ba, wani ma zai yi yadda Babangida ya soke zaben 12 ga watan Yuni kuma ya sha, saboda har yanzu ba a hukunta shi ba. Dole mu tattabar ba a yi hakan ba”, inji.

Tsohon gwamnan Kadunan ya kuma jaddada muhimmancin sauya yadda tattalin arziki, siyasa da al’adu ke tasiri a Najeriya a yanzu.

Ya ce, “Hanyar mafi a’ala tayin haka ita ce tabbtar da ganin Najeriya ta rungumi tsarin gurguzu”.

Sai dai ya ce hakan ba za ta yiwu ba a karkashin tsarin shugaban kasa da ake bi, sai dai a koma tsarin yankuna da firai minista da aka yi amfani da shi a baya.