✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A janye ’yan sandan da ke ba daidaikun ’yan kasa tsaro

Duk da karancin ’yan sandan Najeriya, amma ana tura su wuraren da ba na aikinsu ba, a yi watsi da inda bata-gari da ’yan fashin…

Rahotanni kan yadda ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suke rasa rayukansu a kokarin kare manyan mutane sun zama ruwan dare.

Wannan na faruwa ne sakamakon karuwar ’yan sandan da suke gadi ko ba manyan mutane kariya, wadanda suka hada da ’yan kasuwa da jami’an gwamnati da masu rike da mukaman siyasa da shugabannin addini da ’yan fim da ’ya’yan manya da ’yan rainonsu.

Kowane Sufeto Janar na ’Yan sanda da aka nada yakan bayar da umarnin janye ’yan sandan da suke ba manyan mutane da daidaikun tsaro, amma duk da wannan umarni, al’amura na ci gaba kamar yadda aka saba.

A shekarar 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a janye ’yan sandan da suke kula da manyan mutane, domin a yi amfani da su wajen magance matasalolin tsaro da kasa ke fuskanta, amma sai aka yi wa umarnin nasa kunnen uwar shegu.

A yanzu an fi tura mafi yawan ’yan sanda wuraren da ba aikinsu ba ne.

A watan Fabrairun shekarar 2018, Mataimakin Sufeto Janar Mai Kula da Shiyya ta 5 da ke Benin, Rasheed Akintunde ya koka a kan cewa, kaso 20 ne kawai na ’yan sanda ke ainihin aikin ’yan sanda na kare rayuka da tabbatar zaman lafiya a kasar nan, “inda ragowar kaso 80 suke gadin manyan mutane.”

A rana 11 ga Fabrairun 2018, ’yan kwanaki bayan faruwar haka, sai Hukumar Kula da ’Yan Sanda ta ce, fiye da ’yan sanda 15,000 ne ke kula da manyan mutane a kasar nan ba bisa ka’ida ba.

Duk da bankado wadannan bayanai, an kasa gano dalilin da ya sa har yanzu ’yan sanda suke ci gaba da kula da gama-garin daidaikun ’yan kasa, lamarin da ke jefa su cikin hadari.

Alal misali, mutane bakwai ne waxanda suka hada da ’yan sanda uku da wata mata suka rasa rayukansu a sanadiyar yi wa ayarin Shugaban Cocin Omega Fire Ministries, Fasto Johnson Suleman kwanton bauna, inda ya tsallake rijiya da baya, saboda yana cikin mota mai sulke.

A ranar Lahadi, 11 ga Satumba, mako shida kafin faruwar hakan, ’yan bindiga sun kai wa ayarin Sanata Ifeanyi Ubah hari a Enugwu-Ukwu da ke Jihar Anambra, inda mutum bakwai suka rasu, wandanda suka hada da ’yan sanda biyar.

Mai magana da yawun Ubah ya ce, “Ban da sanatan yana cikin mota mai sulke, da tuni yana barzahu.”

Haka Sufeto Teju Moses mace ’yar sanda ta fuskanci keta haddi daga Farfesa Zainab Abiola, wadda lauya ce mai rajin kare hakkin dan Adam a yayin da take kan aiki, inda ta yi mata jina-jina har ta nemi agajin a kai ta asibiti.

Wadannan abubuwa da suka faru, sun isa su sa hukumomin ’yan sanda su janye duk ’yan sandan da suke ba daidaikun mutane gama-gari tsaro.

Jaridar Aminiya tana Allah-wadai da yadda ake yawan tura ’yan sanda suna ba da tsaro ga daidaikun gama-garin ’yan qasa a daidai lokacin da Najeriya ta fi buqatar ’yan sandan.

Hakan na tava martabar ’yan sanda da kaskantar da su da hana su hidima ga al’umma da tabbatar da dabi’ar nan ta ‘mu am manya’ da kuma rashin hukunta masu matsayi.

Gwamnati na biyan ’yan sanda ne daga kudin shiga da haraji domin kare ’yan qasa ba wasu daidaikun ba.

Haka bai kamata ’yan sanda su riqa ba shugabannin addini da masu kare hakkin dan Adam da ’yan kasuwa kariya fiye da sauran ’yan Najeriya ba.

Saboda haka, bai dace a riqa ba wa mutane kariya fiye da yadda doka ta zayyana ba.

Najeriya tana da ’yan sanda kimanin 371,800, wadanda suka yi matukar kadan.

Amma duk da haka ana tura ’yan sanda wuraren da ba na aikinsu ba, a yi watsi da sauran sassan kasa, inda bata-garin da ’yan fashin daji da ’yan ta’adda suke cin karensu babu babbaka.

Wannan bai dace ba a kasar da take fama da matsalolin tsaro.

Hukumomin ’yan sanda na qoqarin samar da hanyar mayar da ayyukan ’yan sanda na kasuwanci, ta hanyar samar da Shirin Samar da Ayyukan ’Yan Sanda na Musamman.

A watan Agusta, Gwamnatin Tarayya ta hannun Ministan Harkokin ’Yan sanada ta qaddamar da shirin da nufin “tabbatar da aiwatar da al’amura a fili da kuma zage dantse wajen bauta wa ’yan Najeriya”.

Ministan Harkokin ’Yan sanda, Alhaji Muhammad Maigari Dingyadi, wanda ya kaddamar da shirin a Abuja, ya ce Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da shirin tun a watan Yulin shekarar 2021.

Ya kara da cewa, wannan shiri na samar da Runduna ta Musamman zai mayar da hidimomin da ’yan sanda suke yi na kasuwanci, wadanda suka hada da rakiya ta musamman da kuma gadi.

Hakan zai yi hannun riga da Sashi na 214(1) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya sahale samar da Rundunar ’Yan sandan Najeriya.

Sashe na 4 na Dokar ’Yan Sanda ta ba su damar hana laifuffuka da binciko su da kama masu laifi da tabbatar da doka da kare al’ummar kasa da dukiyoyinsu da kuma tabbatar da doka da oda a wuraren da aka dora musu alhaki a ciki da wajen Najeriya.

Dokar ’Yan Sanda da Sashe na 214 (1) na Kundin Tsarin Mulkin 1999 ba su ba da damar samar da wasu ’yan rakiya da masu gadi na musamman ga daidaikun mutane gama-gari ba.

Dole ne a kawo karshen kashe ’yan sanda da kai musu farmaki a yayin da suke kokarin kare al’ummar kasa.

Su kuma masu hannu da shuni da suke sayen motoci masu sulke da nufin kare kansu, ya kamata su biya kungiyoyin tsaro masu zaman kansu domin su kare su, maimakon a rika tura musu ’yan sanda.

Saboda haka, dole a kawo karshen wannan al’ada.