✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kame wadanda suka kashe matafiya a Jos — Buhari

Ba za mu taba yarda da irin wannan kisan gillar ba.

Fadar Shugaban Kasa ta yi Allah wadai da harin da aka kai safiyar Asabar kan wasu matafiya a Jos, babban birnin jihar Filato.

Bayanai sun ce karar kwana ta cimma matafiyan yayin da suke kan hanyarsu ta dawo wa daga wani taron addini da suka halarta a Jihar Bauchi.

  1. Cutar Shan-inna ta sake bulla a Adamawa
  2. An gano karin gawarwakin matafiya 7 a Jos

Cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a daren Asabar, ya ce Fadar Shugaban kasa ta yi bakin cikin samun rahoton kisan gillar da aka yi wa mutane 25 tare da jikkata wasu da dama a wani harin kwanton bauna da aka kai musu.

A cewarsa, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin tsaro da su bankado tare da cafke wadanda suka aikata abin domin su girbi abin da suka shuka a gaban kuliya.

Ya ce Shugaban Kasar ya yaba da kokarin da gwamnonin Filato, Bauchi da Ondo ke yi kan lamarin na ganin wata tarzoma ba ta tashi ba biyo bayan aukuwar lamarin.

Haka kuma, Shugaban Kasar ya yaba wa Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III da Sheikh Dahiru Bauchi da wasu fitattun shugabannin Kiristoci da Musulmai dangane da ci gaba da kokarin kwantar da tarzomar da ke kokarin tashi game da kisan matafiyan.

Fadar Shugaban Kasar wacce ta jajanta wa iyalan wadanda abin ya rutsa da su, ta ce za ta cik gaba da aikin hadin gwiwa da hukumomin yankin, da suka hada da ‘yan sanda da hukumomin gwamnati.

Sanarwar ta ce “An sani cewa Jihar Filato na daya daga cikin jihohin da rikicin makiyaya da manoma ya shafa, amma an yi kokarin kwantar da wutar tarzomar saboda kokarin Gwamna Simon Lalong.

“Wannan ya nuna karara ba rikicin makiyaya da manoma bane, face kisan gilla ga matafiya da suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan halartar abin da ya shafi ‘yancinsu.

“Wannan na nuni da cewar an shirya wa harin, saboda yadda aka farmaki matafiyan.

“Ire -iren wadannan hare-hare a kan ‘yan kasarmu ba za mu yarda da shi ba, kuma ta yi hannun riga da koyarwar manyan addinan al’ummarmu.

“Fadar Shugaban kasa ta tsaya tsayin daka tare da Kiristoci da Musulmai wanda dukkaninsu suka yi Allah wadai da wannan harin kuma ta ba da umarnin bankado tare da cafke wanda suke da hannu a aikata wannan mummunan laifi don yanke musu hukunci.”