✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Kannywood ne zaka ga ’ya’yan da iyayensu suka kasa kula da su – Sarkin Waka

Mawakin ya wallafa wadancan kalaman ne a shafinsa na Instagram

Fitaccen mawakin nan na masana’antar shirya fina-finan Kannywood, Naziru M. Ahmad (Sarkin Waka), ya ce idan ana neman ’ya’yan da iyayensu suka kasa kula da su a zo masana’antar ta fim.

Sarkin Waka ya wallafa hakan ne a shafinsa ma Instagram da Facebook a yammacin Juma’a .

“Ba almajirai ne ’ya’yan da iyayensu suka haifa suka kasa kula da su ba. Idan kana neman ’ya’yan da iyayensu suka haifa suka kuma kasa kula da su, to ka taho masana’antar fim!,” kamar yadda ya wallafa.

Kazalika, mawakin ya yi sharhi kan rubutun nasa da cewa:

“Wannan ita ce gaskiyar malamai ko ta yi dadi, ko kar ta yi dadi.

“Kowa ya dauko sharrinsa sai kan almajirai da iyayensu?

Sakon da Sarkin Waka ya wallafa

“To mu mun san abin da kuke kira almajirci duk da ba sunansa ke nan ba, mun san niyyar da ke iyaye su kai ’ya’yansu mun kuma ga amfaninsa.

“Wato kun fi son a bar yara a daji babu manufa a yi ta basu bindigu suna kashe mu, wannan shi ne burinku? Wannan shi ne kawai, a yi hakuri da mu,” kamar yadda ya wallafa.

Sai dai bisa dukkan alamu rubutun mawakin gugar-zana ne ga wasu, duk da cewar bai bayyana da su wa yake ba ko dalilinsa na yi rubutun ba.

Aminiya ta yi kokari jin ta bakin mawakin, inda ta kira wayarsa amma bai dauka ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya, mawakin ya taba wallafa wani bidiyo kan batun biyan ’yan wasa dubu biyu a matsayin kudin sallama, lamarin da ya tada kura a masana’antar, wanda ta kai ga Furodusa Abubakar Bashir Maishadda, yi masa martani.