✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karo na 5 a 2022, wutar lantarkin Najeriya ta sake daukewa gaba daya

Wannan ne karo na 5 da ta dauke a 2022 kawai

Wutar lantarkin Najeriya ta sake daukewa gaba daya tun daga tushe a ranar Laraba, lamarin da ya jefa ilahirin kasar cikin duhu.

Lamarin na zuwa ne kwana 38 bayan kasar ta fuskanci irin wannan matsalar a ranar 12 ga watan Yuni, kuma kwana 20 bayan Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta kaddamar da wani shiri na musamman na tabbatar da samar da megwat 5,000.

Wannan daukewar, wacce ita ce ta biyar a cikin shekarar nan, ta faru ne wajen misalin karfe 12:00 na rana.

Wajen misalin karfe 11:00 na safe dai, bayanai daga Kamfanin Samar da Lantarki na Najeriya (TCN) sun nuna cewa adadin wutar ya yi kasa daga sama da megawat 3,000 da ake da shi a baya zuwa megawat 2,788.90, wanda aka raba wa kamfanonin samar da wutar guda 19.

Tushen wutar lantarkin gas ta Delta ce dai ta samar da adadi mafi yawa na megawat 453, sai ta Azura da take da megawat 448, yayin da ta Dadin Kowa ta dauke baki daya.

Ya zuwa yanzu dai, manajan da ke kula da wutar a kamfanin TCN bai kai ga bayyana makasudin daukewar wutar ba.