✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Landan Ta Ci Tarar Saurayi Kan Yi Wa Budurwa Dan Kira Landan

Wani matashi ya zama mutum na farko da hukuma ta ci tararsa a Landan saboda yi wa wata mace dan kira a titi. Lamarin ya…

Wani matashi ya zama mutum na farko da hukuma ta ci tararsa a Landan saboda yi wa wata mace dan kira a titi.

Lamarin ya faru ne a kan idon wani dan sanda da ke binciken sirri a Ilford a daren Juma’a.

Daga nan ne kuma ’yan sandan yankin suka zo suka yi a won gaba da shi, kuma aka ci shi tarar Yuro 100.

Hukumomin Birtaniya dai sun ce  wannan ne karon farko da Landan din ta yi amfani da dokar kariyar cin zarafin mai suna PSPO don dakile cin zarafin mata.

Karkashin dokar dai matashin na da kwanaki 28 don biyan tarar, ko kuma ya gurfana gaban kotu ya fuskanci hukuncin zaman gidan yari.

Shugaban Majalisar Dokokin Redbridge, Jas Athwal, ya ce: “Majalisar ta yi rawar gani, kasancewarta ta farko da ta yi amfani da kariyar cin zarafin ta, don dakile mummunar dabi’ar wasu mutanen ta cin zarafin mata a tituna.