✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A karon farko a tarihi, za a fara rabon gado da mata a Jihar Ribas

Gwamnan jihar ta Ribas ne ya sa hannu a kan sabuwar dokar

Gadon dukiya na daya daga cikin abin da iyaye ke bar wa ’ya’yansu idan suka rasu. Sai dai a wasu kabilu na Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, al’adun wasu daga cikinsu sun nuna ’ya mace ba ta cin gadon mahaifinta.

Domin sun dauki ’ya mace kamar wata kayan kyauta ne da idan mutum ya yi babu damar ya waiwaye ta.

A wasu kabilun kuwa, babban wa ne yake handame komai, sai abin da ya so yake tsakura wa kannensa maza ban da mace.

Wannan na da nasaba da cewa ita mace, matar wani ce ko ba dade ko ba jima.

A Jihar Kuros Ribas, akwai kabilar da duk matakin da mace ta kai ba za a ba ta gadon mahaifinta ba.

Haka abin yake a wasu kabilun Jihar Ribas, kuma wannan lamari ne ya sa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya rattaba wa wata doka hannu Mai lamba 4 ta shekarar 2022, da za ta bai wa kowace ’ya mace a jihar damar samun gadon mahaifinta.

Da yake sa wa dokar hannu, Gwamnan ya ce, “Daga yau ya zama doka a rika raba gado da ’ya’ya mata a jihar nan domin ba su ne suka zabi su kasance mata ba, Ubangiji ne Ya zabi hallitarsu a jinsin mata.”

Gwamna Wike ya ci gaba da cewa, “Kada a kara tauye wa mata hakkinsu na gado a raba a bai wa kowace mace nata rabon.”

Wata mata mai suna Naomi Harry, ta shaida wa Aminiya irin yadda ta ji da aka sanya wa dokar hannu.

“Gaskiya na yi matukar farin ciki da Gwamna ya kwato mana ’yancinmu, ya sanya wa dokar nan hannu. Ka ga yanzu mu ma za mu samu hakkinmu na gado da ake hana mu ana barin ’ya’ya maza suna kankane komai. Ana barin mu da aukin zuwa taro da iyali, amma muna matukar farin ciki” inji Naomi.