✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A karon farko Iran ta kyale mata sun kalli kwallon kafa a filin wasa

Sai dai an ware musu kofar shiga filin ta su ta daban da maza

A karon farko a tarihi bayan fuskantar matsin lamba daga hukumomin kwallon kafa na duniya, kasar Iran ta kyale mata sun shiga filayen wasanni don kallon kwallon kafa.

Wasu hotuna da bidiyo dai ranar Alhamis sun nuna daruruwan mata a filin wasa na Azadi da ke Tehran, babban birnin kasar, sanye da kayayyaki da tutocin da ke dauke da launukan kungiyoyin da suke goyon baya.

Sai dai an ware musu kofar shiga filin ta su ta daban don kauce wa cakuduwarsu da maza a kofa daya.

Kazalika, an girke mata masu sa ido da ke sanye da dogayen rigunan da suka rufe musu jiki tun daga kai har kafa a kofofin, don yi wa masu kallon jagora, sannan suna umartar su da su sanya kallabi kafin su shiga.

Bugu da kari, a cikin filayen ma an ware musu wuraren zamansu daban da na maza.

Matan dai sun kalli wasan ne a wata fafatawa da aka yi tsakanin kungiyoyin Esteghlal da ta Sanat Mes Kerman, wadanda shahararru ne a kasar.

Kyale matan su kalli wasan na ranar Alhamis dai na zuwa ne bayan Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) da takwararta ta nahiyar Asiya (AFC), sun yi kira ga kasar da ta kyale matan su fara kallon wasannin a wata wasikar hadin gwiwa da suka aike mata a farkon wannan watan.

Sai dai an sami cin karo da juna daga hukumomin kasar kan ko wasikar ce ta tilasta musu suka amince su fara barin matan su kalli kwallon ko kuma a’a.