✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A kiyayi almubazzaranci lokacin azumi – Buhari ga Musulman Najeriya

Ya kuma roki Musulmai da su yi wa kasa addu’a a watan azumin

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga mawadata a cikin Musulman Najeriya da su kiyayi almubazzaranci lokacin azumin watan Ramadan.

Ya bayyana hakan ne a sakonsa na musamman ga Musulman Najeriya yayin da suke shirye-shirye fara azumin a ranar Asabar, kamar yadda kakakinsa, Malam Garba Shehu ya fitar a cikin wata sanarwa.

Buhari, ya kuma roki Musulman da su yi amfani da lokacin wajen yi wa kasa addu’a kan kalubalen da take fuskanta.

Ya ce azumi lokaci ne da yake ba mutane damar dandana yunwa, kamar yadda talakawa ke ji a kodayaushe, domin su tallafa wa marasa karfi daga cikinsu.

“Musulmai su yi amfani da lokacin wajen horar da kansu da sadaukarwa, wadanda su ne ginshikan gina kowace babbar kasa.

Shugaba Buhari, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su guji almubazzaranci da abinci yayin da wasu suke fama da yunwa, yana mai cewa kamata ya yi su taimaka wa marasa karfi musamman makwabtansu.

Da yammacin Juma’a ce dai mai alfarma Sarkin Musulmai kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya ya sanar da ganin watan a sassa daban-daban na Najeriya.

Hakan dai na nufin Musulman Najeriya za su bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen fara azumin a ranar Asabar.