✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A kiyayi kai wa Musulmi hari da sunan #EndSARS —NSCIA

Majalisar Musulunci ta fusata da masu fakewa da #EndSARS suna cutar da Musulmai a Kudu

Majalisar Koli ta Harkokin  Musulunci (NSCIA) ta fusata kan yadda ake neman amfani da zanga-zangar #EndSARS ana cutar da Musulmai a Kudu.

NSCIA ta fusata da yadda ake fakewa da zanga-zangar a yankin Kudancin kasar ana kai wa masallatai da Musulmi hari haka kawai.

“Sahihan bayanai sun tabbatar cewa Musulman yankin na cikin zullumi saboda barazanar kai musu hari saboda ba addinin Kirista suke yi ba”, inji sanawar Shugaban Kwamitin Watsa Labaran Majalsiar, Femi Abba.

Ya bukaci gwamnonin yankin Kudu da su kare Musulmi duba da harin Babban Masallacin Orlu, Jihar Imo, inda aka kone shi, aka kashe mutum daya, aka jikkata wasu, aka kuma kwashe dukiyoyi ranar Laraba.

Sanarwar ta ranar Juma’a ta kara da cewa muddin aka ci gaba kai wa Musulmi farmaki to hakan ba zai haifar da mummunan sakamako.

Akwai lauje cikin nadi

“Kowa ya san musabbabin zanga-zangar, cin zali da ’yan sanda ke yi ba shi da alaka da addini sannan tsarin mulki ya ba kowa ’yancin addini da ko’ina a kasar”.

Ya ce Majalisar ba ta yi mamakin yadda zanga-zangar ta koma tarzoma ba.

“Hudubobin tunzura da aka rika yi gabanin zanga-zangar ta sa NSCIA zargin akwai wata boyayyiyar manufa ta tayar da rikicin addini”, inji shi.

Kar a kai mu bango

“A karon farko, wannan NSCIA na kashedi ga masu tsauttsauran ra’ayin addini da ke neman yi wa Musulmi cin kashi su shiga taitayinsu.

“Babu wata kungiyar kabila ko addini da ta fi wata zafin kai kuma babu wanda ya fi wani ’yancin yin addini.

“Matsalon siyasa da tattalin arzikin Najeriya sun ishe ta; saboda haka kokarin sanya musu fuskar addini zai jefa kasar cikin bala’i”, inji shi.

Ya kuma bukaci Shugaban ’Yan Sandan Najeirya da ya dakile mummunar barazanar kafin tura ta kai bango domin Majisar ta jima tana kawar da kai game da abubuwa.