✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A lalubi watan Rajab daga daren Juma’a — Sarkin Musulmi

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ta bukaci al’ummar Musulmi da su fara laluben sabon watan Rajab na Kalandar Musulunci daga daren gobe…

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ta bukaci al’ummar Musulmi da su fara laluben sabon watan Rajab na Kalandar Musulunci daga daren gobe na Juma’a.

A wata sanarwa da Majalisar ta fitar wacce ke karkashin jagorancin Fadar Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ta ce Juma’ar ce za ta kasance 29 ga watan Jumadal Akhira wanda zai yi daidai da 12 ga watan Fabrairun 2021.

Sanarwar ta bukaci mutane da su kai rahoton ganin jaririn watan ga wani dagaci ko mai unguwa mafi kusa da su domin isar da sakon ganin jaririn watan ga Sarkin Musulmi.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Wazirin Fadar Mai Martaba Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta ce a a fara duban jijirin watan da zarar rana ta fadi.

Watan Rajab shi ne na bakwai a jerin watannin kalandar Musulunci ta Hijira, wanda daga shi sai na azumin Ramadana.