✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Najeriya aka buga sabbin takardun kudi —Buhari

Buhari ya ce an kara inganta matakan tsaron da ke jikinsu ta yadda buga na jabunsu zai yi matukar wahala.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa a Najeriya aka buga sabbin takardun Naira 200, Naira 500 da kuma Naira 500 da ya kaddamar a ranar Laraba.

Shugaban ya ce Kamfanin Buga Muhimman Takardu na Kasa (NSPM) da ya buga takardun kudin ya kara inganta matakan tsaron da ke jikinsu ta yadda buga na jabunsu zai yi matukar wahala.

“An sanya wa sabbin takardun Nairan karin matakan tsaro da za su yi matukar wahala a iya buga na jabunsu,” in ji shi.

A jawabinsa a lokacin kaddamar da sabbin takardun kudin, Buhari ya ce wadannan na daga cikin dalilan da suka sa ya amince da bukatar Babban Bankin Najeriya (CBN) na sauya takardun kudin.

Ya kuma jinjina wa Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da mataimakansa da suka bukaci tabbatar da sauyin kudaden, da kuma shugabannin kamfanin da ma’aikatansu, “Bisa aikin da suka yi ka’in-da-na’in tare da CBN wajen tabbatar an kammala aikin cikin dan kankanin lokaci.”

A cewarsa, tsarin kudade na duniya ya tanadi a sabunta takardun kudin kasa bayan duk shekara biyar zuwa takwas, amma yanzu kusan shekara 20 ke nan rabon da a yi hakan a Najeriya.

Don haka ya ce lokacin sauya takardun kudin ya dade da yi, amma ba a yi ba.

Ya ce manufar sauye-sauyen sun hada da: “Inganta tsaron kudi, hana buga na jabu, kayyade takardun kudi da ke yawo a hannun jama’a, rage kudaden da ake kashewa wajen kula da takardun kudade da dai sauransu.

“Kamar yadda aka sani dokokinmu na cikin gida — musamman Dokar CBN ta 2007 — ta ba wa ba bankin ikon bayarwa da kuma sauya takardun Naira.

“A kan haka ne a farkon wannan shekara Gwamnan CBN ya gabatar min da wannan bukata, bayan na yi nazarin dalilai da hujjojin da suka bayar na amince,” in ji shi.