✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A shekara 7 Gwamnatin APC ta yi ayyukan da Amurka ta kasa

Fashola ya ce a shekara bakwai Buhari ya samu nasarori fiye da gwmanatin Amurka a bangaren samar abubuwan more rayuwa

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ce gwamnatin jam’iyyar APC ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta samar wa ’yan Najeriya ayyukan more rayuwa da gwamnatin Amurka ta gagara samarwa a shekara bakwai.

Fashola ya ce a shekara bakwai, Gwamnatin Buhari ta samu nasarori a bangaren samar da abubuwan more rayuwa, fiye da na gwamantin Amurka.

Ministan ya ce, “Ina tabbatar muku cewa gwamnatin APC karkashin Shugaba Buhari ta samu nasarar aiwatar da ayyukan da hatta gwamnatin Amurka take kokarin yi a bangaren samar da abubuwan more rayuwa.”

Ya bayyana haka ne a taron jawabin da jam’iyyar APC mai mulki ta shirya da nufin wayar da kan al’ummar Najeriya a kan nasarorin da ta samu a shekara bakwai da ta yi a bisa mulki.

A cewar Fashola, “Ya zuwa watan Disamban shekarar 2021 gwamnatinmu ta kammala ayyukan gina titi da tsawonsu ya kai kilomita 941 a fadin kasar nan.

“A Jihar Kano kadai, alal misali, muna gudanar da ayyukan gina tituna 21, a cikin gari ko sauran garuruwa da kauyuka.

“Wa zai iya tunawa, kafin zuwan gwamnatin APC, yaushe rabon Gwamnatin Tarayya ta gina titi mai tsawon kilomita 50 a kasar nan.

“Wannan shi ne kyakkyawan canjin da muka yi alkawari a 2015 kuma ga shi ana gani a zahiri. Da [’yan adawa] suke ce mu da su babu wata bambanci, gaskiyar magana ita ce, tamu ba irin tasu ba ce.

“Su kudaden gwamnati suke sacewa su kai kasashen waje su boye, mu kuma amfani da kudaden muke yi mu samar da ababen more rayuwa,” inji ministan.

Ya kara da cewa a halin yanzu akwai ayyuka 85o da ma’aikatarsa take gudanarwa da suka hada da gina hanyoyi da gagoji da kuma gidaje a jihohi 34 da ke sassan kasar nan.

Da aka tambaye ministan, ko gwamnatinsu za ta kammala ayyukan da ta faro kafin karewar wa’adin mulkinta a shakearar 2023, sai ya ce, babu gwamnatin da take iya kammala duk ayyukanta; Shi ya sa ya kamata a sake zabar jam’iyyar APC domin ta ci gaba da kyawawan ayyukan da ta da faro.

Game da yawan ciyo bashi da ake zargin gwamnatin APC da yi kuwa, ministan ya ce yin hakan abu ne mai kyau, saboda duk ayyukan da gwamnatin take aiwatarwa suna da muhimmanci.