✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A shirye muke a kashe mu kan ceto ’ya’yanmu —Iyayen dalibai ga El-Rufai

Iyayen sun ce ba mai hana su tattaunawa da ’yan bindiga don su ceto rayukan ’ya’yansu

Iyayen dalibai 39 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su daga Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Jihar Kaduna sun ce za su tattauna da masu garkuwar domin a sako ’ya’yan nasu, tunda gwamnati ta kasa ceto su.

Iyayen sun ce kwana 25 bayan sace daliban, har yanzu ba su ga wani kwakkwaran abin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi domin kubutar da su ba, saboda haka su babu mahalukin da zai hana su tattuauna da masu garkuwar domin a sako ’ya’yan nasu.

Abin da ya sa ake binciken Masarautar Kano kan badakalar filaye

Abin da ya sa ’yan bindiga suke hakon Kaduna – El-Rufa’i

“Muna fada da babbar murya cewa a matsayinmu na iyaye, ba za mu nade hannu mu ki yin komai ba, za mu yi duk abin da za mu iya yi domin kubutar da ’yan’yanmu cikin koshin lafiya.

“Muna jaddada cewa, da yardar Allah, za mu yi duk abin da ba zai gagare mu ba, na ganin ’ya’yanmu ba su halaka ba”, inji mai magana da yawun iyayen daliban, Samuel Kambaia ranar Litinin.

Bayanin iyayen daliban ya biyo bayan gargadin da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi na hukunta duk wanda ta samu yana tattauna da masu garkuwa da mutane.

El-Rufai ya riga ya yi tsayuwar daka cewa Gwamnatin Jihar ba za ta tattauna da ’yan ta’adda ba ko ta biya su kudin diyya ba su sako daliban.

Amma Sakataren kungiyar iyayen daliban, Sanni Friday, ya bayyana cewa su za su tattauna da masu garkuwar ne a matsayinsu na iyaye domin su ceto rayuwar ’ya’yansu, amma ba da yawun gwamnati ba.

Ya ce matukar za a sako musu ’ya’yansu, to su a shirye suke su sayar da yarukanmu ko a tsare su.