✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A shirye muke mu janye yajin aiki —ASUU

Gwamnati kawai muke jira don ko a gobe za mu iya janye yajin aikin.

Kungiyar Malaman Jami’o’i a Najeriya (ASUU), ta ce a shirye take ta janye yajin aikin da take yi don malamai da dalibai su koma makaranta.

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka a tattaunawar da aka yi da shi a Gidan Talabijin na Channels.

Farfesa Osodeke ya ce har yanzu jira suke su ji bayani mai gamsarwa daga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce, “Idan ta ASUU ne, ko gobe ana iya kawo karshen yajin aikin, mun riga mun gama tattaunawa da gwamnati.

“A yanzu da zarar gwamnati  ta kira mu a kan mu zo gobe mu sa hannu a yarjejeniyar da muka kulla, za mu amsa mata.

“Idan gwamnati ta ce mana ta kammala tabbatar da tsarin biyan albashin ma’aikatan jami’a na UTAS, za mu amince sannan mu janye yajin aikin.

“Yanzu jira muke tare da kalubalantar gwamnatin a kan  yaushe za ta rattaba hannu a yarjejeniyar da muka kulla da ita.

“Kuma sai yaushe gwamnatin za ta amince da tsarin UTAS?

“Wadannan su ne tambayoyi biyu da muke bukatar amsarsu daga gwamnatin Najeriya,” inji Osodeke.

Haka nan, ya ce wata biyar kenan da gwamnati ta ki biyan malaman jami’o’in da ke yajin aiki albashinsu.

Ana iya tuna cewa, a ranar 14 ga Fabrairun da ya gabata ne ASUU ta yi yajin aikin gargadi, bayan da wa’adin yajin aikin ya cika ba tare da cim ma bukatunta ba, daga nan ta zarce ta tsawaita wa’adin yajin aikin sosai da kawo yanzu ya ki ya ki cinyewa.