✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

A shirye muke mu yi amfani da Nukiliya a kan Amurka —Koriya ta Arewa

Ya bayyana haka ne a yayin bikin 'Ranar nasara' ta kasar

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya ce a shirye kasarsa take ta yi amfani da makaman kare-dangi na nukilya muddin Amurka ta ci gaba da yi mata barazana.

Ya bayyana haka ne yayin wani jawabi da ya gabatar a matsayin wani bangare na bikin ‘Ranar Nasara’ ta kasar.

Haka nan, shugaban ya yi Allah-wadai da jawaban da Amurka da Koriya ta Kudu suka gabatar albarkacin bikin wannan rana.

Kim Jong Un ya ce duba da barazanar da Amurka ke yi, tana da bukatar taimakon Pyongyang don kafa fannin tsaro mai karfi.

Ya ce, “A shirye sojojinmu suke su tunkari kowanne irin gumurzu, sannan makaman nukiliyar kasarmu a kimtse suke sarai don cika manufarsu.”

Jawabin Kim na zuwa ne bayan da jami’ai a Seoul da Washington suka bayyana cewa Koriya ta Arewa ta kammala shirinta don gwajin makamin nukiliya karon farko tun 2017.

Sai dai kuma, Ministan Harkokin Wajen Koriya ta Kudu ya fada a ranar Laraba cewa, akwai yiwuwar Koriya ta Kudu ta fuskanci takunkumi muddin ta aiwatar da gwajin makamin nukiliyarta.

A jawabin nasa, Shugaba Kim ya ce tun bayan yakin da aka kammala shekaru 70 da suka gabata, Amurka da Koriya ta Kudu na ci gaba da nuna wa kasarsa wasu hali mara kyau wanda akwai bukatar ya dau mataki kan hakan.