A shirye Najeriya take ta taimaka wa Sudan ta Kudu — Buhari | Aminiya

A shirye Najeriya take ta taimaka wa Sudan ta Kudu — Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
    Abubakar Muhammad Usman da Muideen Olaniyi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kudurin Najeriya na tallafawa Sudan ta Kudu kan harkokin siyasa da tattalin arziki.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Addis Ababa, babban birnin kasar  Habasha, yayin wata ganawa ta hadin gwiwa da Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu.

“Najeriya za ta yi duk mai yiwuwa wajen tallafa wa Sudan ta Kudu don samun ci gabanta,” kamar yadda mai Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina ya fitar a wata sanarwa ranar Talata.

Shugaba Buhari ya kuma jadadda yunkurin Najeriya na kawo daidaito da ci gaba da nahiyar Afrika baki daya.

Ya nemi hadin kan kasashen da suka ci gaba don samar da abubuwan bunkasa rayuwa kamar ilimi, tattalin arziki, harkar lafiya da sauransu.

Dangane da halin da ake ciki a kasar Guinea da Mali kuwa, Buhari ya sake nanata cewa dole ne shugabannin kasashen Afirka su goyi bayan kokarin da ake yi na dawo da mulkin dimokuradiyya a kasashen.

Shugaban ya nuna damuwa cewa muddin kasar Libiya ba ta samu kwanciyar hankali ba, za a ci gaba da samun yaduwar makamai a yankin Sahel.

A nasa jawabin, Shugaba Kiir, wanda ya amince da rawar da Najeriya ke takawa a Afirka, ya yaba da kokarin kasar a fafutukar kwato ‘yancin Sudan ta Kudu.

Ya kuma yaba wa Uwar-gidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari kan yadda ta taimaka wajen ilimantar da ‘yan matan kasarsa da dama.

“A yammacin Afirka, ECOWAS na shiga tsakani a duk lokacin da wata kasa ta samu matsala. Yakamata a karbe hakan a Gabashi da Tsakiyar Afirka,” in ji shi.

Shugaba Buhari da shugaba Kiir na daga cikin shugabannin Afirka da suka halarci bikin rantsar da Firaminista Abiy Ahmed na Habasha, a karo na biyu.