✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A takaice: Bitar labarun makon jiya

Zanga-zangar iyayen dalibia kan gwajin COVID-19 Wasu iyayen daliban ajin karshe a makarantun sakandaren kudi na kwana a Jihar Ogun sun yi bore kan neman…

Zanga-zangar iyayen dalibia kan gwajin COVID-19
Iyaye a lokacin da suke bore kan kan kudin gwajin COVID-19 ga dalibai

Wasu iyayen daliban ajin karshe a makarantun sakandaren kudi na kwana a Jihar Ogun sun yi bore kan neman su biya N25,000 na gwajin COVID-19 ga kowane dalibi.

Iyayen sun kai ’ya’yan nasu domin gwajin ne kafin bude makarantu ga dalibai masu kammala sakandare a ranar Talata 4 ga watan Yuli, kamar yadda ya jihar ta shardanta.

Daga baya gwamnatin jihar ta soke biyan kudaden ta kuba ba wa iyayen daliban hakuri.

Ga cikakken labarin yadda iyaye daliban suka yi boren

2023: Mun amince mulki ya koma Kudu —Arewa

Matasan Arewacin Najeriya sun yi fatali da kiran da dan wan Shugaban Buhari ya yi cewa jam’iyyun siyasar kasar su yi watsi da tsarin mulkin karba-karba su bi cancanta.

Shugaban kungiyar matasan mai rajin wanzar da tsaro da zaman lafiya, Salisu Magaji, ya ce a bari mulki ya koma yankin Kudu a zaben 2023 domin tabbatar da dunkulewar kasar a mulkin demokradiyya.

Karanta cikakken labarin na Matasan Arewa na goyon bayan mulki ya koma Kudu.

Harin Boko Haram ba zai hana ni magana ba —Zulum
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum

Gamnan Borno, Babagana Zulum ya ce ba zai taba yin shiru ba kungiyar Boko Haram na kashe mutanen jihar.

Gwamnan wanda kungiyar ta kai wa hari a ranar Laraba 29 ga watan Yuli, ya ce alkawarin da ya yi wa Allah a ranar 29 ga Mayu, 2019 shi ne kare mutanen Borno, don haka dole ya damu idan an taba rayuwarsu.

“Alkawari ne tsakanina da Allah. A matsayina a gwamna ba zai yiwu ba in yi shiru ana ta kashe wasu daga cikin mutum milliyan shida da ke jihar ba”, inji shi.

Latsa nan domin karanta labarin cikakke.

Babban Shaihin Darikar Tijjaniya ya kwanta dama

Allah Ya yi wa babban malamin darikar Tijjaniya kuma Babban Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass, Sheikh Khalifa Ahmad Tijjani bin Sheikh Ibrahim Abdullahi Inyas, rasuwa.

Shaihin malamin ya rasu ne a kasar ta Senegal a daren Lahadi 2 ga Agusata bayan ya yi fama da jinya.

Kafin rasuwarsa shi ne shugaban mabiya darikar Tijjaniyya wadanda aka kiyasta sun kai kusan miliyan 100 a fadin duniya.

Rikicin biliyoyin Dala tsakanin APC da PDP

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kalubalanci jam’iyyar hamayya ta PDP da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, da su yi bayanin kwangilar Dala miliyan 460 da gwamnatin PDP ta bayar domin sanya kyamarorin nadar bayanai ta bidiyo a shekarar 2010 ba tare da an yi aikin ba.

Sai dai a martanin da PDP ta bayar ta ce neman “shashantar da zargin da ake wa APC na neman jinginar da Najeriya”, ya tabbatar cewa akwai kanshin gaskiya a zargin da ake wa APC. Galabarin irin cacar bakin da ya barke tsakanin APC da PDP.

Mun kashe miliyan N523 kan ciyar da dalibai
Sadiya Umar Farouk

Sanawar cewa shirin ciyar da dalibai a jihohi uku a lokacin kullen COVID-19 a Najeriya ya lakume Naira miliyan 523.3, ya tayar da kura.

Ministar Agaji da kyautata rayuwa Sadiya Farouk, ta ce an aiwatar da shirin ne a jihohi uku bayan rufe makarantu a ranar 29 ga watan Maris.

Ga cikakken labarin yadda ta ce ciyarwar ta lakume miliyan N523.

’Yan Kaduna sun yi wa El-Rufai raddi
Gwamnatin Jihar Kadduna ta sauya tsarin dokar kullen coronavirus Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai

Gwamnan Kaduna Nasir El-rufa’i ya ce akwai yiwuwar dawo da dokar kulle saboda karuwar masu kamuwa da COVID-19 a jihar.

Hakan ta sa ‘yan jihar mayar da martani ga gwamnan cewa illlar kullen ta fi ta cutar girma. Sun ce tun farko kakaba kullen bai samu shawarwarin wandanda suka dace ba, tare da kira gare shi da ya dakatar da yunukurin.

Karanta yadda ’yan jihar suka yi masa raddi a nan.

#RevolutionNow: Jami’an tsaro sun kama mutum 60 a Abuja
Masu zanga-zangar #RevolutionNow

Jami’an tsaro sun kama masu zanga-zangar lumana ta #RevolutionNow akalla 60 a Abuja, babban birnin tarayya.

Masu zanga-zangar lumanar na bin titunan manyan biranen jihohin kasar nan ne domin tuna zagayowar shekara guda da gudanar da zanga-zangar lumana ta farko ta #RevolutionNow, wadda aka yi  a ranar5 ga watan Agusta, 2019.

Wanda ya shirya gangamin, Omoyele Sowore, a shafinsa na Twitter ya ce jami’an tsaro sun ci zarafin masu zanga-zangar lumanar a Legas.

Mahara sun kashe mutum 30 a Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe akalla 20 a harin da suka kai daren Laraba a Karamar Hukumar Zankon Kataf ta Jihar Kaduna.

Mutane da dama sun bace bayan harin na kauyukan Apyiashyim, Atak’mawai, Kibori, da kuma Kurmin Masara a Masarautar Atyap.

‘Makusancin Ganduje ya ci kudaden malamai’
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano

Hukumar karbar korafi da hana cin hanci da rashawa ta Jihar Kano na bincike handame kudaden da ake wa mai taimaka wa gwamnan jihar, Ali Baba Agama-Lafiya.

Ana zargin Ali Baba da karbe N45,000 daga cikin N50,000 da aka raba wa alarammomi da suka yi wa jihar addu’o’i kan matsalolin tsaro da na annobar COVID-19.

Ga cikakken labarin a nan. Latsa don karantawa.

Bayan kulle za mu fara yajin aiki —Jami’o’i

Jami’o’i sun yi barazanar fara yajin aiki da zarar an bude su saboda matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa tsakaninsu da gwamnati.

Ma’aikatan jami’o’in sun ce sun gaji da jan kafar gwamnati wajen biyan bukatunsu na gyaran albashin da makarantun bayan yarjejeniyar da suka yi. Karanta cikakken abun da ya faru a nan.

INEC ta bude shafin duba sakamakon zabe

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bude shafin duba sakamakon zabe ta intanet domin ingantawa tare da yin komai a fili.

Kwamishinan hukumar mai kula da yada labarai da wayar da kan jama’a, Festus Okoye ya ce dama can “INEC ta kosa ta rika yin komai a fili a harkar zaben Najeriya, musamman wajen bayyana sakamako.

Ga Cikakkane labarin Sabon shafin INEC na duba sakamakon zabe ta intanet.

Zaben Edo: Ize-Iyamu ya karbi tutar takara
Shugaba Buhari yana mika wa Ize-Iyamu tutar takarar jam’iyyar APC

Shugaba Buhari ya mika wa Osagie Ize-Iyamu tutar tsayawa takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaben Jihar Edo.

Buhari ya ba shi tutar ne bayan ganawarsu a Fadar Shugaban Kasa gabanin kaddamar da yakin neman zaben Ize-Iyamu a ranar Asabar.

Latsa nan domin karanta cikakken labarin

Aisha Buhari ta tafi kasar waje neman magani

Matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta fice zuwa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa domin neman magani.

Aminiya ta gano cewa Aisha Buhari na fama da ciwon wuya tun bayan dawowarta daga Legas inda ta je ta’aziyyar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, wanda cutar coronavirus ta yi ajalinsa.

Karanta cikakken labarin a nan

Ya kamata mulki ya koma kudu a 2023 – El-Rufa’i
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce kamata ya yi mulki ya koma yankin Kudu idan Shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023.

A hirarsa da Sashen Hausa na BBC, El-Rufai ya ce ko da yake tsarin na karba-karbar ba doka ba ce yana da kyau a mutunta shi tun da yankunan kasar sun yi na’am da shi.

Domin karanta cikakken labarin sai a latsa nan.