✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A tarihin Najeriya babu shugaban da ya fi Buhari yaki da talauci —Lai Mohammed

Ya ce tun da aka kafa Najeriya ba a taba wani shugaba da ya yaki da talauci kamar Buhari

Ministan Watsa Labaran Najeriya Alh. Lai Muhammad ya ce tun da aka kafa Najeriya ba a taba wani shugaba a tarihi da ya samar da shirye-shiryen yaki da talauci kamar shugaba Buhari ba.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron gwamnonin arewacin Najeriya da aka gudanar a Kaduna.

“Gwamnatin shugaba Buhari ta bullo da shirye-shirye irinsu N-Power, TraderMoni, MarketMoni, tallafi ga manoma ta hanyar shirin Anchor Borrowers, rabawa masu karamin karfi tallafin N5,000 a kowanne wata da dai sauransu,” inji Lai Mohammed.

Ministan ya ce shirye-shiryen da aka bullo da su, sun ta’allaka ne ga taimakawa matasa da sama musu ayyukan yi da kawar da talauci a tsakanin mata da matasa a kasar.

Taron ya samu halartar manyan shugabanni da masu rike da sarautun gargajiya na Arewacin Najeriya, kuma ya gudana ne karkashin jagorancin gwamnan jihar Kaduna kuma mai masaukin baki, Malam Nasir El-Rufa’i.