A wajen dan sanda na sayi bindiga saboda na rika kare kaina – Matsafi | Aminiya

A wajen dan sanda na sayi bindiga saboda na rika kare kaina – Matsafi

‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga
    Hameed Oyegbade, Osogbo da Sani Ibrahim Paki

Wani matsafi da ake zargi da mallakar bindiga a Jihar Osun mai suna Tajudeen Olalekan, ya ce a wajen wani jami’in dan sanda ya sayeta saboda ya rika kare kansa.

Ya ce ya sayi bindigar ne a wajen wani dan sanda mai suna Haruna Yusuf.

An dai yi bajekolin Tajudeen da Harunan ne da kuma wasu mutum biyar a hedkwatar ’yan sandan Jihar da ke Oshogbo, babban birnin Jihar, bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma shiga kungiyar asiri.

A cewar dan sandan, ya saci bindigar ne da ke aiki a caji ofis dinsu, sannan ya sayar da ita ga shugaban matsafan.

Ya ce a sakamakon batan bindigar, an kori jami’in daga bakin aiki, lamarin da ya jefa shi cikin matsananciyar damuwa, daga bisani kuma ya mutu a sakamakon haka.

Sauran wadanda aka yi bajekolin nasu sun hada da  Chukwudi Eze da Alebo Elijah da Abimbola Olanipekun da Alebo Israel da kuma Olarinre Abiodun.

Tajudeen ya ce lokacin da aka daga likafarsa zuwa shugaban kungiyar tasu ta matsafa, ya sayi bindigar daga hannun dan sandan saboda ya rika kare kansa.

Sauran makaman da samu daga wajen wadanda ake zargin sun hada da bindigu kirar gida da na waje kala daban-daban har kala biyar da harsasai guda 11 da wukake guda biyar da gatura uku da kuma adda guda daya.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Olokode Olawale, ya ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu don su girbi abin da suka shuka.