✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A wata uku an kashe mutum 323, an sace 949 a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta ce an kashe ’yan bindiga 64 a musayar wuta a wata ukun farkon 2021.

Akalla mutum 323 ne aka kashe cikin wata uku a fadin Jihar Kaduna. 

Gwamnatin Jihar ta ce an yi garkuwa da kimanin mutum 949 daga watannin Janairu zuwa Maris na 2021.

Kwamishan Tsaron Harkokin Cikin Gidan Jihar, Samuel Aruwan ya shaida wa taron zangon farkon 2021 kan sha’anin tsaro cewa jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 64 yayin artabu a fadin Jihar.

Ya ce Mazabar Kaduna ta Tsakiya ita ce ke da mafi yawan mutanen da abun ya shafa idan an kwatanta da sauran gundumomin da ke Jihar.

“A cikin mutane 323 da aka kashe, maza 292 ne, mata 20, sai kananan yara 11.

“Mutum 236 da aka yi wa kisan gillar an yi musu ne a Kananan Hukumomin Birnin Gwari, Chikun, Igabi, Giwa, da Kajuru.

“An kashe mutum 77  Birnin Gwari, Chikun mutum 52, Igabi  45, Giwa 42, sai Kajuru mutum 20, duk a wata ukun farkon wannan shekarar.

“A Mazabar Kudancin Kaduna kuma an kashe mutane 68; wadanda biyar daga  cikinsu mata ne ’yan kasa da shekaru 18.

“A Karamar Hukumar Kajuru na kashe mutum 28, Zangon Kataf mutum 14, Kagarko 12.

“Arewacin Kaduna shi ne mafi karanci wurin yawan mutanen da aka kashe —mutane 19, inda Zariya ke da kaso mafi yawa na mutum shida da abun ya ritsa da su a yankin,” a cewarsa.