A watan Maris ’yan mata za su koma makaranta a Afghanistan – Taliban | Aminiya

A watan Maris ’yan mata za su koma makaranta a Afghanistan – Taliban

Kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid
Kakakin Taliban, Zabihullah Mujahid
    Sani Ibrahim Paki

Gwamnatin Taliban ta kasar Afghanistan ta ce ’yan mata da ke karatu a kasar za su koma makaranta nan da watan Maris mai zuwa.

Wannan ne dai mataki na farko da zai share fagen sake komawar ’yan matan makarantu tun bayan da kungiyar ta karbe mulkin kasar a watan Agustan bara.

Kakakin gwamnatin kasar, kuma Mataimakin Ministan Al’adu da Yada Labarai, Zabihullah Mujahid, ne ya tabbatar da haka lokacin da yake jawabi ga ’yan jarida ranar Asabar.

Ya ce Sashen Ilimi na gwamnatin kasar ya yanke shawarar sake bude makarantun ga ’yan mata daga farkon sabuwar shekarar kasar, wacce za ta fara aiki daga ranar 21 ga watan Maris na 2022.

Ko da yake Taliban ba ta haramta ilimin ’ya’ya mata ba a hukumance, amma ta rurrufe makarantun sakandiren ’yan mata tare da hana su zuwa jami’o’in gwamnati a wasu sassan kasar.

Mata dai a kasar ba sa samun wuce matakin aji bakwai a Firamare a kasar tun bayan fara mulkin kungiyar a kasar, kuma yunkurin dawo da hakan ma daga cikin muhimman abubuwan da masu rajin kare hakkin mata da kungiyoyin kasa da ke ta kokarin ganin an yi tsawon watanni.

“Ilimin mata yana da muhimmanci a wajenmu, muna kokarin ganin mun magance abubuwan da suka yi masa tarnaki nan da sabuwar shekara, ta yadda za mu sake makarantu da jami’o’i,” inji Zabihullah.

Har yanzu dai hukumomin kasa da kasa na jan kafa wajen amincewa da gwamnatin da Taliban ke jagoranta a matsayin halastacciya, saboda fargabar za ta sake kakaba dokoki masu tsauri, kwatankwacin irin wadanda ta yi zamanin mulkinta, shekara 20 da suka wuce.

A lokacin dai, an haramta wa mata zuwa makarantu, yin aiki ko kuma cakuda da maza a wuraren taruwar jama’a.

“Mu ba ma adawa da ilimin mata,” lokacin da yake jawabi a sakatariyar Ma’aikatar Al’adun Kasar.

“A larduna da dama, mun sake bude azuzuwan matan, amma a wasu yankunan da aka rufe, an yi haka ne saboda dalilai na tattalin arziki, amma muna kokarin magance matsalolin,” inji shi.

Tuni dai aka fara kyale matan da suka wuce matakin aji bakwai su fara komawa makarantu a larduna kusan 12 daga cikin 34 da ke kasar.