✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A Yammacin Alhamis za a raba jadawalin Gasar Zakarun Turai na 2022/23

A kowace shekara akan fitar da kungiyoyin kwallon kafa 32 na nahiyar Turai, gwargwadon irin Kokorin da kowaccensu yi a kakar wasannin da ta gabata.…

A kowace shekara akan fitar da kungiyoyin kwallon kafa 32 na nahiyar Turai, gwargwadon irin Kokorin da kowaccensu yi a kakar wasannin da ta gabata.

A kan zakulo kungiyoyi hudu-hudu daga sassan kasashen Turai a kowace shekara domin fitar da jadawalin da za a fafata a Gasar Zakatun Turai.

Hakazalika akan saka kungiyoyin a cikin tukane hudu, wato a kowace tukunya akwai kungiyoyin wasanni guda takwas.

A wannan shekarar a tunkunyar farko akwai kungogin wasanni kamar haka:

  1. Real Madrid
  2. Frankfurt
  3. Man City
  4. Milan
  5. Bayern
  6. Paris
  7. Porto
  8. Ajax

Tukunya ta biyu:

  1. Liverpool
  2. Chelsea
  3. Barcelona
  4. Juventus
  5. Atlético
  6. Sevilla
  7. Leipzig
  8. Tottenham

Tukunya ta uku:

  1. Dortmund
  2. Salzburg
  3. Shakhtar Donetsk
  4. Inter
  5. Napoli
  6. Benfica
  7. Sporting CP
  8. Leverkusen

Tukunya ta hudu:

  1. Rangers
  2. Dinamo Zagreb
  3. Marseille
  4. Copenhagen
  5. Club Brugge
  6. Celtic
  7. Plzeň
  8. Haifa

Bayan kammala wannan hadin jadawalin da za a yin na kungiyoyi 32, za a fara buga wasannin cikin rukuni Gasar Zakarun Turai daga ranar 6 ga watan Satumba zuwa 10 ga watan Yunin 2023.