✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A yi adalci tsakanin makarantun hukuma da na kudi

Yajin aikin da malaman makarantun Firamare na Jihar Kaduna suka fara yi a makon farko na sabuwar shekara abu ne wanda ya  nuna wa duniya…

Yajin aikin da malaman makarantun Firamare na Jihar Kaduna suka fara yi a makon farko na sabuwar shekara abu ne wanda ya  nuna wa duniya cewa gwamnatin Jihar ba da gaske take yi ba game da sasanta tsakaninsu, har hakan ya bayar da damar inganta matsayin koyarwa kamar yadda take  ikirari. Al’amarin koyarwa a makaranatun Firamaren Jihar Kaduna ya shiga cikin wani mawuyacin halin tun farkon hawan  Gwamna Nasir el-Rufa’i shekaru biyu da  rabi da suka gabata.  Tun daga wancan lokaci hankulan daliban makarantun firamare da na malamamansu da kuma na iyayensu ba su kwanta lami lafiya ba, kullum akwai wata sabuwar fitinar da ake takalowa, wacce ke kara sa yanayin da ake ciki na dada tabarbarewa, kuma bisa ga dukkan alamu za a dade ba a gano bakin zaren warware  matsalolin da ke tasowa ba. Ba wani abu ba ne kuwa ya janyo haka illa kokarin nuna gwaninta da kuma ba-ni-na-iya wadanda Gwamna ke  ta gwadawa a kokarinsa na jwagwalgwala al’amura da niyyar gyaran da ya kasa yi, hakan kuma ya zame wa kowa jangwam.  

Da farko dai Gwamna Nasir bai tashi daukar matakan yin gyara ga harkokin ilmin da ya tabarbare ba sai duk kuwa da cewa yana sane da cewa akwai matsaloli masu yawan gaske, wadanda gwamnatinsa ke zaune a bisansu, kuma idan da a lokacin ya tashi haikan da nufin gyarawa fisabilillahi ba abin da zai hana shi samun nasara. To amma sai ya tsaya yana ta tsilla-tsilla da tsugudidi, yana daukar matakan da shi kansa ya san cewa ba za su kai ga mafita ba, sa’annan kuma ya ki jin shawarar kowa sai abin da zuciyarsa kawai ta raya masa. A game da haka ba a jin kan kowa sai na Gwamna Nasir, shi ne ke  kidansa, shi ne  kuma ke taka rawarsa, shi ne   gwani-na-gwanaye, wanda ya fi kowa sanin yadda za a tunkari batun tabarbarewar ilmi da na mulki,  shi ne  kuma kuma ya fi kowa nakaltar  dabarun warware matsalolin da ya haddasa  da sunan gyara irin na gangar Abznawa.  

Matsalar koyarwa a Jihar Kaduna da ma sauran  jihohin kasar nan ba  a dare guda suka girma  ba kamar shuri, saboda haka nan  mawuyacin abu ne a ce za a kawar da su tashi guda, kuma ba tare da an bi salsalar afkuwarsu ba da neman shawarwari da taimakon dukkan masu ruwa-da-tsaki a wannan al’amarin. Shi ya sa ake gani waran-gwankin da Gwamna Nasir el-Rufa’i yake yi don kawo gyara, har yana bugun kirji yana tutiya cewa domin ceto matsayin  harkokin koyarwa da suka tabarbare ne a  Jihar Kaduna,  zai ci gaba da gamuwa da cikas iri-iri domin kuwa manufa da burinsa na yin haka ba shi ne inganta matsayin ilmi ba, shi abin da ya sanya a gaba shi ne yadda zai kyautata harkokinsa na siyasa  da kuma tara dukiyar  da za ta ba shi damar  kashe gararin gabansa nan gaba.

Wannan ne dalilin da ya sa tun farkon hawansa mulki ake ta samun kiki-kaka a harkokin bayar da ilmi,  har sai da ta kai an bar makarantun babu ingantattun kayayyakin aiki, cikin wani irin yanayi na rashin gyaran da ke kara tabbatar da yadda aka bari suka tabarbare, sa’annan kuma aka bar malaman makarantun kara zube, ba wanda ya damu da irin matsin da suke ciki sakamakon rashin samun sukunin gudanar da aikinsu yadda ya kamata. 

A irin wannan yanayin ne Gwamnatin el-Rufa’i ta addabe su da yawan bincike don tantance sahihancinsu a  bakin aiki, aka dakatar da yawa daga cikinsu ba tare da biyansu albashi ba, ba  kuma ce  da su ga makomarsu ba.  Haka nan aka yi ta yi fiye da shurin masaki, aka  kuma kasa kawo karshen al’amarin da ya rigaya ya karya wa malaman gwiwowi ya kuma raunana musu zuciya, inda daga karshe kuma daliban da suke koyarwa ne matsalolin suka fi shafa.    

Malaman ba su san cewa sa’ilin da suke kukan targaden da gwamnati ta yi musu za su kuma yi na karaya ba, domin kuwa gwamnati ta shafa wa fuskarta bula, ta ce dukkansu manyan jahilai ne kuma dakikai, wadanda ba su nakalci ilmin koyar da ‘yan aji hudu na firamare ba. Saboda haka nan sai ya aka ce wajibi ne malamai sama da dubu talatin da biyu su zauna jarrabawar da za ta nuna kwarewa da cancancartarsu, su kuma samu maki saba’in da biyar cikin dari kafin a amince da su. Malaman dai ba su yi kasa a gwiwa ba, sun zauna waccan jarabawar da sakamakonta ya zamanto abin zambo ga gwamnatin da ta shirya ta. Hakan  ya nuna cewa son kai da biye zuciya aka yi, domin an yi amfani da jarrabawar ce wajen aikata masha’ar da gwamna ke so na korar malamai ala-kulli-halin.

Gwamna Nasir el-Rufa’i ya bukaci maye guraben wadancan malaman da wasu sababbi daga cikin dubu arba’in da uku da su ma suka zauna wata jarrabawar da ake cewa ta yaudara ce, kuma a daidai wannan  lokacin ne malaman suka kai kara kotun kare hakkin ma’aikata don ta bi bahasin korar da ake cewa an yi wa wasunsu, kotun kuma ta bidi gwamna ya dakatar da waccan manufar har sai ta gama bin bahasin kukan malaman a gabanta. Kowa ya yi tsammani cewa Gwamna Nasir, a matsayinsa na wanda ya yi amanna da tafarkin dimokuradiyya, kuma mai bin doka da aiki da oda, zai bi umurnin kotu, amma kash! Sai ga shi nan ya yi abin da ko wani dan-tasha ma  ba zai yi ba, domin kuwa ya doddode kunnuwansa, ya kuma muzanta umurnin waccan kotun yana mai  cewa  bakin alkalami ya bushe,  umurnin kotu ya yi latti, domin ‘aikin gama ya gama.’ A ina aka taba cewa umurnin kotu ya yi latti idan ba a tsari irin na Malam Nasir ba, mai tsananin sani? 

To tun da malaman makarantu ba su da wani galihun da ya wuce kotu da kuma ‘yancin  tafiya yajin aiki don neman hakkokinsu yadda ya kamata, kungiyar NUT ta malaman ta fara yajin aiki a ranar Litinin takwas ga watan nan, wanda ya biyo bayan na somin tabin da aka yi tun lokacin da aka fara dauki-ba-dadi tsakaninta  da gwamnati. Bisa ga dukkan alamu kuma iyayen yara na goyon bayan malaman domin kuwa ba su zumudin tura ‘ya’yansu makaranta har sai an kai ga samun ingantacciyar maslaha game da al’amarin. 

Yanzu dai abin da ake gudu game da haka ya rigaya ya afku, an jefa harkokin koyarwa a Jihar Kaduna cikin mawuyacin hali don tsabar neman suna da tsananin son iyawa. Wadannan ne dalilan da suka kai Gwamna Nasir dukufa yin wala-wala da ilmin ‘ya’yan talakawa  a Jihar Kaduna sa’ilin da  takwarorinsu na wasu jihohi ke ci gaba da karatu  ba wata matsala. Idan domin  a taimaki ‘ya’yan talakawa da ke karatu a makarantun gwamnati ne ake yin haka,  yaran da ke karatu a makarantun kudi fa, su   ba ‘ya’yan talakawan Jihar Kaduna ne ba? Ai su ma suna da hakki  kan wannan gwamnati na ganin an inganta yanayin  koyar da su a makarantun da suka gwammace aikewa da ‘ya’yansu.  Ya  kamata   gwamnati  ta yi adalci ta kuma tabbatar ba ta  da  gefe a  harkar koyarwa tsakanin makarantun hukuma da  masu zaman kansu.