✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘A yi wa Abba Kyari afuwa ko da an same shi da laifi’

Kungiyar ta ce mutum tara yake bai cika goma ba

Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (AYCF) ta yi kira ga Hukumar Aikin Kula da Ayyukan ’Yan sanda da daukacin masu ruwa-da-tsaki a dambarwar da ta shafi fitaccen dan sandan nan Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda (DCP) Abba Kyari, su yi masa adalci da afuwa ko da an same shi da laifi domin a cewarsu mutum tara yake bai cika goma ba.

Kungiyar ta nemi a dubi kyawawan ayyukan da ya gabatar a baya wajen yakar manyan miyagun masu garkuwa da mutane da ’yan damfara da sauran bata-gari.

Shugaban Kungiyar Matasan ACF, Alhaji Yarima Shattima ya shaida wa Aminiya cewa za su yi duk abin da za su iya na goyon bayan Abba Kyari tare da tabbatar da ganin an yi masa adalci.

Ya kara da cewa Abba Kyari hazikin dan sanda ne matashi dan Arewa wanda yake kare martabar kasa.

“Ko a baya-bayan nan matsalar da ta tunkaro kasar nan ta ’yan bindiga a Kudu maso Gabas da suka yi ta kashe ’yan sanda suna kone kadarorin gwamnati, DCP Abba Kyari aka tura kuma cikin ikon Allah a kasa da mako biyu ya kawo karshen matsalar wacce a baya ta fara addabar kasar nan.

“Ba mu ce kada a bincike shi ba fatarmu ita ce a yi masa afuwa a kuma yi waiwaye a kan ayyukan alherin da ya gabatar a baya, idan aka same shi da laifi,” inji shi.

Alhaji Yarima Shattima ya ce ba sa goyon bayan a mika wa kasar Amurka Abba Kyari domin Hukumar FBI ta bincike shi, “Domin Najeriya kasa ce mai cin gashin kanta kuma laifin da ake zarginsa da shi a Najeriya aka ce ya yi.”

Mutaimakin Kwamishinan ’Yan sanda Abba Kyari ya samu kansa ne a cikin wannan dambarwa bayan zargin da fitacceen dan damfarar nan na duniya Abbas Ramon da aka fi sani da Hushpuppi ya yi cewa ya ba shi cin hanci domin ya kama abokin harkallarsa.

Ramon Abbas ya amsa laifin damfarar wani dan kasar Katar Dalar Amurka miliyan 1.1.

Tuni dai hukumar ’yan sanda ta bada umarnin dakatar da DCP Abba Kyari domin a gudanar da bincike a bisa zargin da ake masa, inda aka maye gurbinsa da DCP Tunji Disu.