✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A’a, kada a kara kudin lantarki

Watakila za a iya cewa sanarwar da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC), ta yi a kwanakin baya – lokacin taron shekara-shekara na…

Watakila za a iya cewa sanarwar da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC), ta yi a kwanakin baya – lokacin taron shekara-shekara na nazari Kan Dokar Kudin Lantarki na kara kudin lantarkin ya zama na lallai; sai dai an yi ta ce a lokacin da bai dace ba sam.  Da take sanar da shirin karin da take son yi a watan Afrilun bana, hukumar ta yi ikirarin “Za ta nazarci yanayin kasuwar lantarkin ta fuskar dawainiyar samar da shi da makamantansu a bara da kuma a yanzu.”

NERC ta bayyana cewa: “Shirin Gwamnatin Tarayya na Ceto Harkar Makamashi da aka sabunta bai yi nuni da kara kudin wutar nan take ba – har sai 1 ga Afrilun bana, kuma sai a karshen shekarar 2021 karin zai fara aiki gadan-gadan. A farko, Gwamnatin Tarayya ce za ta himmatu ainun wajen cike gibin harajin da za a samu A tsakanin dawainiyar samar da lantarkin da kuma cajin da za a yi wa jama’a.” Muhimmin furuci daga bayanan da Hukumar NERC ta yi shi ne “Dalilan da za su haifar da ainihin kudin da za a biya na wutar.” Wadannan dalilan sun hada da na farashin gas, wanda samar da shi tare da bukatarsA a kasuwannin duniya ke da tasiri a kansa da canjin kudaden waje kan Naira da hauhawar farashi – wanda har yanzu yake kan digo biyu, sai kuma samar da makamashin – da shi ma har yanzu yake mizanin kasa sosai. idan aka yi la’akari da wadannan dalilai, to lallai ne a ce kari ya zama tilas!

Kodayake, batun rage radadin shi ne Hukumar NERC ta ce nufi da ‘cajin da ya dace – wato dai kudin da zahirin abin da mai amfani da wutar lantarki  zai iya biya. Idan da a ce abubuwa suna tafiya daidai, to ya kamata kowane bayan wata shida a sake nazartar Dokar Kudin Lantarki – amma rabon da a yi haka tun shekarar 2016. Hakan ya faru ne sakamakon lalacewar al’amura a harkar. Mafi yawan hankoron da aka gindaya wa kamfanonin Samarwa da na Rarraba Lantarkin (DISCOs da GENCOs) a tsarin sayar musu da lantarkin ba su iya cimma musu ba. Alal misali, ya kamata a ce karfin lantarkin da ake samar wa ya kai megawatt dubu 12 zuwa yanzu – amma ko kusa. A daya hannun kuma, ya kamata a ce akalla wutar da ake rarrabawa ta kai megawatt dubu bakwai, zuwa yanzu. Amma maimakon haka, har yanzu karfin lantarkin da ake rabawa yana hawa da sauka tsakanin megawatt 3,000 zuwa 3,500; yayin da wadda ake samarwa kuma take kan matakin megawatt 5,000. Wadannan tarin matsaloli, masu karya gwiwa ne ga masu amfani da lantarki da masu zuba jarin kansu.

Koke-koken da ake yi na kin jinin karin a fadin kasar,  ba sa rasa nasaba da rashin wadatar lantarkin da ake raba wa jama’a, sakamakon yadda galibin mutane suke ganin ba su gamsu da irin lantarkin da ake ba su bai kai kudin da suke biya ba. Batun nan na kiyasta kudin lantarki wanda har yanzu ba a warware shi ba, na ci gaba da yi wa yanayin illa. Kodayake, kiyasta kudin wuta ka iya zama ya dara ko ya gaza. Sai dai, ’yan Najeriya sun fi samun tsawwalawa a kiyasta kudin wutar da suke biya. Mutanen da gidajensu babu mitar lantarki, kan fuskanci cajin lantarkin na fitar hankali wanda yake abin haushi wasu lokuta. A karkashin irin wannan yanayi, kara kudin ka iya zama marar tabbas kuma wanda babu hujjar yin sa.

Abu ne mai kyau da Gwamnatin Tarayya ta rattaba hannu da Kamfanin Siemens na kasar Jamus, wanda ya goge a harkar  kwangilar samar da ababuwan da ake bukata wajen fadada samarwa  da rarraba lantarki. Idan dai aka aiwatar da tsarin yadda ya dace, aikin da kamfanin na Siemens zai gudanar, shakka babu zai bunkasa samar da hasken lantarki a Najeriya. Mun jinjina wa gwamnati sakamakon daukar wannan mataki. Kodayake, muna goyon bayan matsayar da Majalisar Wakilai ta dauka inda ta yi kira ga Ma’aikatar Makamashi ta jingine batun karin kudin lantarkin “Har yanzu akwai dimbin tambayoyin da suke bukatar amsa.” Ko shakka babu, kamfanonin rarraba lantarkin, (DISCOs), za su yi ta hura wuta ga Hukumar NERC wajen ganin ta kara kudin, domin kawai su kara samun kudaden shiga. A bayyane take, idan har za a samar wa dukkan mutane mitar lantarki, kamfanonin DISCOs za su kara samun kudin shiga ta hanyar tabbatar da suna kula kai-tsaye da miliyoyin abokan huldarsu a Najeriya. Domin haka, zai zamana karin kudin ya zama mai ma’ana yayin da aka samar w ajama’a da yawa mitar wuta; bugu da kari, samar da lantarkin ya zama a-kai-a-kai kuma a wadace. Hukumar NERC da na DISCOs da GENCOs da sauran masu ruwa-da-tsaki a harkar, ya kamata su mayar da hankali kan wannan bangare, maimakon karin kudin a daidai lokacin da samarwa da raba lantarkin ya yi matukar karanci.