✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba Gida-gida ya yi barazanar kauwarace wa yarjejeniyar zaman lafiya a Kano

Sai dai shugaban APC, Abdullahi Abbas, ya ce an murde zancen nasa ne, amma shi bai furta kalaman harzukawa ba.

Dan takarar Gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-gida), ya yi barazanar kaurace wa rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiyar da ake shirin yi a jihar.

Abba ya ce muddin ba a kamo Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas an hukunta shi ba, to fa ba da shi za a rattaba hannu a yarjejeniyar ta zaman lafiya a jihar ba.

Wannan na zuwa ne duk da APC a jihar ta bukaci dole a hukunta shugabannin NNPP a jihar saboda zargin kai wa mambobinta hare-hare a jihar.

Abba Gida-gida ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, a lokacin da yake tsokaci kan batun da aka danganta da shugaban APC na jihar, Abdullahi Abbas game da rikicin zabe.

Dan takarar ya ce muddin ba a dauki wani mataki a kan, ba shi da zabin da ya wuce na janyewa daga rattaba hannu a yarjejeniyar da ake shirin yi a jihar.

Dan takarar ya yi zargin ’yan APC sun yi wa mambobin jam’iyyarsa da dama rauni sakamakon rikicin da ya yi zargin dan Shugaban APC ya jagoranta.

Sai dai kuma, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Gwamna na APC a Kano, Muhammad Garba, ya ce mambobin NNPP ne suka kai harin a lokacin da suka bi Abban zuwa wajen wani daurin aure da ya halarta a yankin Karamar Hukumar Gwale.

Ya kara da cewa, abin takaici ne yadda dan takarar na NNPP ke dora alhakin rikicin a kan APC, har da neman a kama Shugaban jam’iyyar.

Shi ma Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Umar Haruna Doguwa, ya jaddada cewa za su kaurace wa yarjejeniyar zaman lafiyar.

“Jama’a muke wakilta, don haka ba za mu nade hannu mu zuba ido wani na fada mana abin da ya ga dama ba. Wannan karon, a shirye muke da duk abin da za su zo da shi.

“Kowa ya san mu da son zaman lafiya a Kano, amma abin damuwa shi ne yadda mambobin APC suka furta kalaman harzukawa a gaban jami’an tsaro ba tare da an dauki wani mataki a kan hakan ba,” kamar yadda fada a cikin hirarsa da Sashen Hausa na BBC.

Sai dai shugaban APC, Abdullahi Abbas, an murde zancen nasa.

A cewarsa, “Kalmar ‘Tsiya-Tisya’ ba tana nufin kai wa wani hari ba ne,  amma matse kaimi don cin zabe.”