✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abduljabbar: Kotu ta ba da izinin hana shi wa’azi da rufe masallacinsa

Umarnin na hana sanya karatunsa a kafafen yada labarai ya fara aiki nan take.

Kotu ta ba wa Gwanmantin Jihar Kano izinin rufe masallacin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kuma hana sanya karatuttukansa a kafafen yada labarai a Jihar nan take.

Mai Shari’a Muhammad Jibrin na Kotun Majisatare da ke zamanta a Gidan Murtala, ta kuma umarci Gwamnatin Jihar da ta hana da malamin daga gabatar da wa’azi ko yin duk wani lafazi da ke iya haddasa fitin.

Umarnin kotun, wanda Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Wada A. Wada ya nema na zuwa ne washegarin ranar da Gwamantin Jihar ta dauki makamanciyar matakin bisa zargin malamin da cin zarafin Sahabban Manzon Allah (SAW) da neman tayar da fitina a karatutukan da yake gabatarwa a majalisinsa na Masallacin As-habul Kahfi da ke jihar.

Kotun ta umarci Gwamnatin Jihar ta rufe masallacin na Sheikh Abduljabbar da ke Filin Mushe nan take har sai jami’an tsaro sun kammala binciken da suke gudanarwa a kan zargin da ake yi wa malamin.

Ta kuma wajbata wa jami’an tsaro tabbatar da bin umarnin sau da kafa tare da sanya kafar wando da suka wanda aka samu yana kalamai marasa kan gado da ke iya tayar da zaune tsaye a Jihar Kano.