✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abduljabbar ya nemi kotu ta ba shi damar kare kansa ba tare da lauyoyi ba

Yana zargin lauyoyin ne da karancin ilimin addinin da za su iya kare shi.

An yi musayar yawu a Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano inda ake ci gaba da sauraron shari’ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara kan zargin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W)

Yayin da aka dawo zaman kotun dai ranar Alhamis, Sheikh Abduj]ljabbar ya dage kan cewa kotun ta ba shi dama ya kare kansa ba tare da lauyoyi ba.

Bukatar hakan ta taso ne sakamakon zargin gazawar da yake yi musu saboda rashin kwarewarsu a fannin ilimin addinin Musulunci, musamamn bangaren Hadisi.

Ana dai tuhumar Abduljabbar Kabara da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma laifin tayar da hankulan jama’a.

Abduljabbar Kabara ya shaida wa kotu cewa bai gamsu da yadda lauyansa ya yi wa shaida na farko tambayoyi ba a lokacin zaman da ya gabata, don haka yake neman kotu a wanann karon ta ba shi dama ya yi tambayoyi da kansa ga shaida na biyu.

A zaman kotun na ranar Alhamis, bangaren masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Suraj Sa’ida ya gabatar wa kotu shaida na biyu wani mai suna Murtala Kabir Muhammad wanda malamin makaranta ne kuma mazaunin unguwar Kofar Na’isa Lungun Makera wanda kuma yana daya daga cikin daliban Abaduljabbar din.

Lokacin da aka zo yi wa shaida tambayoyi ne sai lauyoyin Abduljabbar suka nemi kotu ta ba wa shi damar ya yi tambayoyin ga shaida inda suka yi dogaro da sashe na 36 (6d) na Kundin Tsarin Mulkin Kasa na shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.

Sai dai Alkalin Kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya yanke hukunci akan takaddamar, inda ya ba malamin ko dai ya kare kansa shi kadai, ko kuma ya bar lauyoyinsa su kare shi.

Hakan ya sa Abduljabbar din ya zabi kare kansa inda su kuma lauyoyinsa a nasu bangaren suka ce suna nan daram a cikin shari’ar musamman ma duba da cewa ba za a iya ci gaba da shari’ar ba tare da lauyoyi ba tun da shari’ar babban laifi ce wanda za a iya yanke hukuncin kisa a kanta.

Su ma a nasu bangaren masu kara sun ce duk da cewar ba su da suka akan Abduljabbar din ya kare kansa, amma sun tunatar da kotun cewa shari’ar babban laifi dole sai da lauyoyi ake yin ta don haka akwai bukatar a sake duba batun ficewar lauyoyin Abdulljabbbar daga shari’ar.

Daga nan kotun ta dage zamanta zuwa ranar 11 ga watan Nuwamban 2021 don ba wa dukkanin bangarorin shari’ar damar sake yin nazari akan batun tare da samo hanyar warware shi don ci gaba da shari’ar.