✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da kasafin Buhari na karshe zai kunsa

Kasafin Naira tirilian 19.76 da Buhari zai gabatar shi ne karshe a wa'adinsa na biyu da ke karewa ranar 29 ga watan 2023.

A safiyar Juma’a Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar wa Majalisar Dokoki ta Tarayya daftarin kasafin shekarar 2023 na Naira tiriliyan 19.76.

Kasafin da Buhari zai gabatar shi ne na takwas a mulkinsa, kuma na karshe a wa’adinsa na biyu da ke karewa ranar 29 ga watan 2023.

Tun a ranar Laraba aka tsaurara matakan tsaro a zagaye da harabar Majalisar domin karbar bakuncin shugaban kasan da ’yan rikayarsa a ranar Alhamis.

An takaita shiga harabar Majalisar a ranar Alhamis ga masu takardar izini na musamman da aka yi wa ’yan jarida da jami’an tsaro da ma’aikata.

Kazalika an umarci ma’aikatan Majalisar da ba su da alaka aikin kasafin da su zauna a gida ranar Alhamis.

A halin yanzu dai kowanne daga Majalisar Dattawa da ta Wakilai suna zama ne a zauren wucin gadi, kasancewar ana aikin gyaranta.

Bayan ya gabatar da kasafin ga zaman hadin gwiwar Majalisar Dattawa da ta Wakilai, kwamitocinsu za su fara aikin tantancewa da neman bahasi daga hukumomi da ma’aikatu kan kason da aka ware wa kowannensu.

Idan suka kammala babban zauren Majalisa zai mika wa bangaren shugaban kasa bayan yin nazari da sauye-sauye, kafin daga karshe shugaban ya gabatar da kasafin kudi na karshe, wanda idan Majalisa a amince zai sanya hannu a kai.

Ana sa rai kamar yadda aka yi a bana, badi ma za a fara aiwatar da kasafin daga watan Janairu.

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar mayar da lokacin kasafin kudi daga watan Janairu.

Kasafin shekaru 7 da suka gabata sikeli

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa a kasafin kudi bakwai da Buhari ya gabatar a baya masu gibi ne,  ta yadda abin da ake shirin kashewa ya zarce kudaden shiga da gwamnati ke hasashen samu a shekara.

Abubakar Aliyu, masanin tattalin arziki kuma jami’in huldar hada-hadar hannun jari ya ce, idan aka yi kasafi mai gibi, to sai an nemo ko an ciyo bashi domin kudaden da za a cike gibin da aka samu.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka na Jami’ar Bayero ta Kano, ya ce, “Tun da Buhari ya zo, kudin da ake samu [a gwamnati] bai kai wanda ake kashewa ba; saboda haka duk shekara sai ka ji za a karbo bashi saboda za a cike kasafin kudi.”

Ya ce Buhari yana irin wannan kasafi ne bisa fahimtar mazhabar tattalin arziki da ke ganin ita ce hanyar bunkasa tattalin arziki, “Idan Allah Ya sa an dora kasafin a kan bangarorin tattalin arziki da za su kawo cigaba da bunkasa masana’antu da harkar noma da sauransu, wadanda su ne idan an bunkasa su arziki zai rika zagayawa [tsakanin jama’a].

“Idan ka tabbatar za ka samu N100 sai ka yi lissafin N150, to idan ka samu N120 to ka ka ga N20 da at shigo ba ta cikin lissafinka, jajircewarka da takura wa kanka ne ya sa ka samu.”

Amma ya ce, irin wannan kasafi da bashi ake cike shi, domin daga karshe kasafin da aka yi doka yake zama, don haka sai an an aiwatar da shi, “Hakan ne ya kai kasar ga halin irin bashin da ke kanta yanzu.”

Abubakar Aliyu, ya ce, shi ya sa, “Tun da farko mun mamakin ganin ana kasafi na tiriliyoyin Naira alhali kasar ba ta iya samun wadanann kudade.

“To a hankali ana cike gibin nan da basussuka, har yanzu aka kai ga a shekaru bakwan nan, basussukan da aka rika karba ana cikin gibin sun zo sun durkusar da kasa.”

“Hakan ya sa a rubu’in farko na wannan shekara an biya bashi da kudaden da muke samu a cikin gida, har ma sai da aka kara da ciyo bashi na kashi 120 cikin 100,” in ji masanin tattalin arzikin.”

Ya bayyana cewa a tsawon shekara bakwai da suke gabata, “Ahin tsoro shi ne kudaden da aka ciyo bashi domin manyan ayyyuka, zan iya cewa ba yi ayuukan ba, kuma kudaden babu su.

“Na san bashin da aka karba na Dala biliyan 5.5 a hanyar sayar da hannun jarin Euro Bond domin gyaran tashar wutar lantarki at Mambilla da gyaran filayen jiragen sama da biyan ‘yan kwangila.

“Amma daga baya Ministan Lantarki ya fito yana cewa ko share filin ba a yi ba.”

Bangaren da ya fi samun kaso

Masanan sun bayyyana cewa, bangarorin tsaro, manyan ayyyuka, abubuwan more rayuwa da noma, da masana’anu. su ne suka fi samun kaso mai tsoka a kasafin shekaru bakwai da suka gabata.

Farfesa Sheka ya ce, Buhari ya ba da fifiko a kan bangaren noma ne, saboda “ana so a ciyar da kai, an rufe boda saboda a irin karfin da za a iya noma shinkafa da sauran abubuwa.

“An fito da abubuwa da dama, kamar ba wa manoma wani bashi, kyauta-kyauta wanda bankin CBN a jagoranta,” a cewar Farfesa Sheka.

A cewar Abubakar, wani bangaren da ya samu kaso mai tsoka shi ne bangaren gudanar da gwamnati, wanda a cewarsa bai kamata ba, “yaya za a yi ka karba basuka ka yi wananna abubuwan da su?”

Bangaren tsaro ya samu kaso mai tsoka ne saboda matsalolin da kasa ke fuskanta ta wannan bangare, kama daga ta’addancin Boko Haram zuwa ‘yan bindiga da ‘yan aware da sauransu.

Batun manyan ayyuka kamar yadda suka bayyana ya samu kaso mai yawa ne saboda ayyukan gina titunan jirgin kasa da hanyoyi, “wadanda ga su nan ana ta yi.”

Basussuka da tsare-tsaren tallafi da ake bayarwa ga matasa da masu sana’o’i da masana’antu, na daga cikin abin da ya sanya ake bai wa bangaren abubuwan more rauwa kaso mai tsoka.

Shin kwalliya ta biya kudin sabulu?

Abubakar Aliyu ya ce kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba a kasafin shekaru bakwai da suka gabata.

Yaki da talauci

Game da tsarin bayar da rance ko tallafi, ya ce, “Abin mamaki shi ne babu wani tsari, ana cewa za a yi yaki da talauci.

“Yaki da talauci ba wannan hanya za a bi ba. Yaya za ku bai wa mutane ba ku ba tura su wurin sana’a ba, kuna ba su kudi, idan ma kudaden na isa hannunsu ke nan,” in ji shi.

Noma

Farfesa Sheka ya ce akwai sauran rina a kaba a bangaren noma, domin duk da tallafi da rance da sauran matakan da gwamnati dauka kan ganin an ciyar da kai, “Sai ya zama wadda ake nomawa a gidan nata neman ko ma ta fi da wajen tsada, ko kuma nana kan-kan-kan.

“ Ka ga a iya cewa ba a ci nasara ba, domin ana noma ta a gida, amma farashi bai sauka ba, sai dada hauhauwa ma yake, har ana maganar da za a bude boda shigo da ta wajen, talakawa su samu sauki, da ya fi.”

Manyan ayyuka

Game abubuwan more rayuwa, malamin jami’an ya bayyana cewa hakika ana yi, “Amma more rayuwar ba ta zo ba, saboda mmfanin mutun ya gina abu shi ne ya yi amfani da shi.”

Amma a cewarsa, duk da cewa Buhari ya dora a kan gina titin jirgin da Gwamnatin Jonathan ta fara, kuma yana gina tituna, rashin tsaro a kan hanyoyin sufurin tamkar an yi baya babu zani ne.

“Babban abu shi ne bayan an sanya abu kuma a mora… ana yi amma wannan rashin tsaro ya sa mutane sun shiga cikin zullumi, wasu abubuwan ma ba a gane cewa an samar da su.

“Yawancin wannan rashin tsaron ya goge abin da aka yi mai kyau. Kowa zai ce ai in za ka tafi kana tsoro, in za ka dawo kana tsoro,” inji shi.

Kasafin 2023

Da yake hasashen abin da kasafin 2023 zai kunsa, Abdullahi Aliyu, ya ce, ya na ganin ba za ta sauyya zane ba, lura da abin da aka saba gani a kasafin shekarau bakwai da suka gabata.

Sai dai ya ce babu mamaki, “A kara wa bangaren zartarwa kaso saboda bukatun gudanar da gwamnati da na siyasa kamar yin zabe da sauransu.”

kason da aka ware na ciyo bashi domin cike gibin ya wuce kashi 3 cikin 100 da aka kayyade, ya kai kashi biyar cikin 100 na tattalin arziki na cikin gida.

“Ita kanta Ministar Kudi ta fada cewa wannan kashi biyar ne cikin 1oo, sun wuce ma da kashi biyu, wanda ka ga sun karya wanna kai’da gaba daya.

Ya kara da cewa, “Za a gabatar da kasafin Naira tiriliyan 19, wanda a ciki kusan tiriliyan 12 bashi ne za a je a karba.