Daily Trust Aminiya - Abin da ke jawo tabarbarewar tsaro a kasar nan – Sheikh Abub
Subscribe

Sheikh Abubakar Giro Argungu

Abin da ke jawo tabarbarewar tsaro a kasar nan – Sheikh Abubakar Giro Argungu

Ranar Juma’a 28 ga Yuni ne fitaccen malamin addinin Musulunci nan, Sheikh Abubakar Giro Argungu ya ziyarci Jihar Kuros Riba domin bude Masallacin Juma’a da al’ummar Musulmin Awi a Karamar Hukumar Akamkpa suka gina. Wakilin Aminiya ya zanta da malamin kan matsalolin  tsaro da suka addabi Arewa da Najeriya, inda ya ce, su a fahimtarsu miyagun ayyukan da ake yi ne ya yi tsanani kuma shi ake zaton ya kawo fitina a Najeriya:

Malam matsalar tsaro ta dabaibaye wasu jihohin Arewa da  Najeriya, ga satar mutane domin neman kudin fansa da satar shanu da kai hare-haren ta’addanci a wasu kauyukan jihohin Arewa maso Yamma kuma ga matsalar Boko-Haram me Malam zai ce a nan ?

To fahimtarmu ta gefen almajirai a Najeriya ta saba wa fahimtar yawan mutane don mu fahimtarmu ita ce miyagun ayyukan da muke yi a Arewa sun yi tsanani. Farkon abin da ya kawo fitina a Najeriya, idan ka dubi makabartunmu yadda ake cire gawarwaki ana tsafe-tsafe da su ka dubi yadda yara ke bacewa ake fada a Rediyon Najeriya na Kaduna kullum ana fada duk matsafa suke dauke su.

Idan ka duba irin ta’addancin da ake yi da Alkur’ani kamar abin da ya faru a Zamfara takardun Kur’ani bakwai aka samu cikin masai da ire-irensu. Ita Borno a karan kanta a da kowa ya san muna yara wuri ne da idan ana son a haukata wani ko a kashe wani ko a masa tsafi galibi akan ce a je Borno. Mu dai mun ba da laifin ga miyagun ayyukanmu domin Kur’ani ya fadi cewa Allah ba Ya canja ni’imar da mutane suke kanta sai miyagun ayyukansu sun canja ta. Na biyu, ana bukatar masu amana daga bangaren gwamnati domin dole mu yarda cewa, talauci ya yi tsanani a Arewa. Wannan na cikin abin da ya bayar da gudunmawa wajen samar da rashin tsaro. Abin da ya fi illa shi ne a Arewa akwai karancin ilimi, inda kashi 75 cikin 100 na jama’ar Arewa matasa ne ba su da ilimi na addini ko na boko mu da muke yawo cikin kauyuka muka san yadda al’amarin yake.

Kabilar da ta fi tsanani a wajen bangaren da ya shafi sace mutane idan ka duba a Arewa, kabila guda ce ita kuma wannan kabila idan ka duba an yi watsi da iliminta za ka iya samu cikinsu su ne suke da manyan malamai a cikinsu amma ba wani tsari da gwamnati ta bi na samar musu da hanyoyinsu na neman ilimi ne ta hanyar kirkiro da shirin gwamnati na bayar da ilmi ga ’ya’yan makiyaya (Nomadic Education) amma kuma zaluntarsu kadai aka rika yi.

Baya ga haka kotunanmu na kauyuka suna cin amanarsu tsakani ga Allah, suna yi musu shari’a ta fitina kwarai inda suke kwace musu shanu, suna cutar da su. Mun san da wannan ba su jin dadin alkalai, manoma da kansu in wani dalili ya sa Bafulatani ya samu matsala da wani manomi aka kashe shi sai a kama Bafulatani 30 a zo a kashe su. Don haka abin da zan ce akwai gyaran da gwamnati ya kamata ta yi.

Wane gyara Malam zai so gwamnatin ta yi?

Ah! Yaya za ka tura masu yaki da miyagun mutane kuma ba ka ba su cikakken kudi ba? Idan ka duba Gwamnatin Tarayya ta yi kokari tana tura sojoji da ’yan sanda, ina nufin kananan ’yan sanda da kananan sojoji, idan ka duba kananan ’yan sanda mobayil da sauransu masu shiga cikin daji, nawa gwamnati take ba su? Dole ne idan ana son aikin nan ya yi yadda ake so, tsakani da Allah, ba makamai kawai za a ba su ba, a dauki nauyinsu yadda ya kamata wannan shi zai taimaka musu, su tsaya su yi aikinsu tsakani da Allah. Mu mun san kananan sojoji suna cikin wahala, mun san ’yan sanda na cikin wahala kuma su ne ake bukatar su yi yaki a madadin gwamnati dole sai an gyara wannan .

  Masallacin Juma’a na garin Awi a Kuros Riba

Mece ce shawarar Malam ga gwamnati tun daga matakin tarayya zuwa jihohi?

Shawarata ga gwamnatin Najeriya shi ne abin da ya shafi tsaro a irin wadannan kasashe a yi kokari a yi amfani da kananan mutane wajen samun bayanai na sirri kada a je gari ana son a san sirrin gari a nemi uban kasa ko Sarki, ko Shugaban Karamar Hukuma, ko wani Gwamna ko Sanata. Galibin irin wadannan mutane Abuja ce garin zamansu koyaushe a nemi mutanen karkara, a tura mutanen da ba a iya gane siffarsu, su samo sirri daga mazauna kauye, su za su ba da sirrin yadda yakin nan yake da kuma yadda za a yi yakin nan a yi nasara ba wai wadanda suke zama a Abuja ba, manyan mutane. Ba wai a ce an tura Sufeto Janar, bayan an tura Minista waye zai je karkara cikin daji? Ba zai je ba, sai dai zai iya ziyartar Sarki ko wani uban kasa ko Sanata da nufin halartar wani biki shi k enan su koma Abuja.

A je can cikin daji ko kauye a samu sirrin abin nan da kuma inda mutanen nan suke, wallahi kauyawa sun san inda mutanen nan ke zama idan yaki ake yi kuma abar amfani da kafofin watsa labarai. Bai yiwuwa a gaya min inda maboyar ’yan Boko Haram take ko an gaya min inda masu garkuwa da mutane suke in dauko rundunata zan je wurin yaki kuma in shiga gidan rediyo in yi sanarwa za mu shiga dajin Zamfara ai shi ke nan an ba su damar guduwa  ba a shirya yaki ba.

Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) ya koyar da yadda za a yi yaki kuma ya yi galaba bai da bindiga, bai da motocin yaki amma kuma ya yi yaki kuma ya yi nasara, yayin da  bai da abin hawa kamar jiragen sama kuma ya yi nasara dole ne a tambayi hanyar da ya bi ya samu nasara  a wadannan abubuwa.

More Stories